Siyasa

Kwankwaso: NNPP Ba Ta Da Ƙawance da Kowace Jam’iyya a Hali Yanzu

Jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya tabbatar cewa jam’iyyarsu tana cikin kwanciyar hankali, kuma a halin yanzu babu wata jam’iyya da suke da haɗin gwiwa da ita.

A jawabin da ya yi a wajen taron majalisar ƙoli na NNPP da aka gudanar a Abuja, Kwankwaso ya bayyana cewa ƴaƴan jam’iyyar ba sa yin gaggawa wajen yanke hukunci.

“Ƴaƴan jam’iyyarmu ba sa gaggawa. Komai muna yinsa a hankali,” in ji shi.

Ba a fara tattaunawa da kowace jam’iyya ba

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ƙara da cewa, kawo yanzu ba su fara tattaunawa da kowace jam’iyya ba domin ƙulla ƙawance. Sai dai ya bayyana cewa nan gaba za su iya shiga tattaunawa idan buƙata ta taso.

“Mu ƴan siyasa ne, kuma a shirye muke mu tattauna da duk wanda ke son tattaunawa da mu,” in ji Kwankwaso.

Maganar komawa APC

Tun bayan zaɓen 2023 ake ta rade-radin cewa Kwankwaso zai iya komawa jam’iyyar APC, musamman lokacin da ake hasashen zai samu mukamin minista. Wannan ya biyo bayan furucin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa zai yi aiki tare da wasu daga cikin ƴan hamayya a gwamnatinsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks