Wasanni

Labaran Kwallo: Sergio Reguilon zai haɗe da Messi a Inter Miami, Arsenal ta kafe kan Yildiz

Tsohon dan wasan baya na Tottenham da Manchester United, Sergio Reguilon, yana tattaunawa da Inter Miami kan yiwuwar komawa gasar MLS domin hadewa da Lionel Messi bayan kwantiraginsa da Spurs ya ƙare a bazara. (Mail)

Chelsea ba za ta nemi Marc Guehi na Crystal Palace ba, duk da cewa dan wasan baya ɗan Ingila mai shekaru 25 zai bar ƙungiyar kyauta a bazara mai zuwa. (Express)

Sai dai Chelsea na da sha’awa ga dan wasan gaba Antoine Semenyo na Bournemouth, kuma tana shirin biyan fam miliyan 78 don ɗan wasan Ghana mai shekaru 25. (Fichajes)

Juventus ta ƙi tayin fam miliyan 58 daga Chelsea kan ɗan wasan gaba Kenan Yildiz, ɗan Turkiyya mai shekaru 20. (TuttoJuve)

Haka kuma, Arsenal na ci gaba da zawarcin Yildiz, inda ta tura wakilai domin kallonsa a wasan Juventus da AC Milan ranar Lahadi. (Tuttosport)

Joshua Zirkzee na Manchester United, mai shekaru 24, zai fi son ci gaba da wasa a Premier League idan ya bar Old Trafford, inda Everton da West Ham ke sha’awarsa. (Talk)

James Ward-Prowse (30) na shirin barin West Ham a bazara, bayan da ya rasa dama a karkashin sabon kocin Nuno Espirito Santo. (FootballInsider)

Ronald Araujo na Uruguay ya ƙi barin Barcelona, inda ya sanar da Chelsea, Liverpool, Tottenham da Juventus cewa yana son ci gaba da zama a ƙungiyarsa. (Sports Espanya)

Sai dai Barcelona na iya tilasta sayar da shi a watan Janairu, bayan da ta saka masa farashin fam miliyan 35. (Fichajes)

West Ham na neman ɗan wasan gaba Endrick na Real Madrid a matsayin aro, amma za ta fuskanci hamayya daga Valencia da Real Sociedad. (Fichajes)

Arsenal na fatan sabunta yarjejeniya da Bukayo Saka (24) a lokacin hutun ƙasashe domin tabbatar da ya ci gaba da zama ɗan ƙungiyar. (TBR Football)

Liverpool kuma na ci gaba da tattaunawa da Ibrahima Konate (26) kan sabuwar yarjejeniya, duk da cewa Real Madrid na zawarcin ɗan wasan na Faransa. (FootballInsider)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks