Gwamnan Zamfara ya Sabon Sarkin Katsinan Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin Sabon Sarkin Katsinan Gusau na 16.
Wannan naɗin ya zo ne bayan rasuwar mahaifinsa, Mai martaba Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Yuli, 2025. Alhaji Abdulkadir, wanda kafin naɗin sa ya kasance Bunun Gusau, shi ne babban ɗan marigayin sarki.
A cewar sanarwar da Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu, an bi dukkan tanade-tanaden doka wajen tabbatar da sabon sarkin Katsinan Gusau. Haka kuma an girmama zaben da masu zaɓen sarkin suka yi bisa doka.
Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna, inda ya bukace shi da ya jajirce wajen jagoranci na gari, tare da bin sahun kyawawan halayen da iyayensa suka kafa a masarautar.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai da ci gaban masarautar Gusau, jihar Zamfara da ƙasa baki ɗaya, yana mai cewa sabuwar rawar da sabon sarkin zai taka za ta kasance muhimmiyar dama wajen bunƙasa al’umma.