KannyWood

Maishadda: “Burin da nake da shi yanzu shi ne na fitar da Kannywood zuwa duniya!”

Daya daga cikin fitattun furodusoshin Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda, ya bayyana manyan burikansa da irin nasarorin da ya gani a cikin masana’antar fina-finai. Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Hadiza Gabon a cikin shirin ta na “Gabon’s Room Talk Show.”

A cikin hirar, Maishadda ya tabo batutuwa da dama – daga burin sa a masana’antar, har zuwa albarkar da ya ce tana cikin harkar fina-finai idan aka yi amfani da ita yadda ya dace.

“Idan ka samu kanka a cikin wannan masana’anta ba tare da ka amfana da romon arzikin da Allah ya ajiye a cikinta ba, to guda biyu ne: ko dai dama ta zo maka amma ba ka amfana da ita yadda ya kamata ba, ko kuma ba ka yi abin da ya dace ba a lokacin da ya dace,” in ji Maishadda, wanda ya shafe fiye da shekaru 15 yana daukar nauyin fina-finai.

Dalilin da ya hana shi halartar bikin Rarara da Aisha Humaira

Da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa ba a gan shi a bikin daurin auren mawaki Dauda Kahutu Rarara da Amaryarsa, Aisha Humaira, Maishadda ya ce tafiya zuwa birnin Legas ce ta hana shi halartar taron.

“Bikin Rarara da Aisha Humaira, tamu ce. A gaskiya ni ne sanadin haduwarsu tun da fari. Mun taba yin waka tare da Rarara inda na dauki nauyin wakar. Bayan mun kammala, na bukaci a yi reposting a dandalin sada zumunta. Aisha Humaira na daga cikin wadanda suka yi hakan,” in ji shi.

Ya kara da cewa wannan damar ce ta bude kofar hadin gwiwa tsakaninsu.

“Na nuna wa Rarara irin yadda ta dage wajen yada wakar. Sai na bukaci a sanya ta a wata waka da muka shirya, domin a lokacin kamar kawata ce. Daga nan muka yi wakar ‘Dogara Ya Dawo’ tare.”

Alaƙarsa da Umar M. Sharif

Dangane da jita-jitar da ke yawo cewa alakar Maishadda da mawaki/actor Umar M. Sharif ta tabarbare, ya bayyana cewa ba gaskiya ba ce.

“Ba a ganin Umar a cikin ‘Gidan Sarauta’ zango na hudu ba yana nufin akwai matsala. A shirye-shirye masu dogon zango, sau da yawa ana cire jarumai sannan daga baya su dawo. Don haka babu wata matsala a tsakanina da Umar,” in ji Maishadda.

Yaushe aure da Nana Firdausi?

Ana ta rade-radin cewa yana da niyyar aure da jarumar fina-finai Nana Firdausi, duba da yadda suke yawan fitowa a fina-finai tare.

“Eh, muna aiki da juna sosai. Na yarda da kwazonta. Duk wani aiki da muka yi tare, tana nuna cikakken hazaka da kishin aiki. Amma har yanzu babu wani batu na aure a tsakanina da ita. Fahimta ce ke tsakaninmu,” in ji shi.

Burin Maishadda: Fita da Kannywood zuwa duniya

Maishadda ya bayyana babban burinsa a yanzu da cewa yana fatan ya fitar da fina-finan Kannywood zuwa kasashen waje, musamman India.

“Ina son in zama furodusa na duniya – wato ‘International Producer’. Ba zan tsaya a Najeriya kawai ba. Ina burin yin fim a India, kasar da ake samun riba sosai a harkar fina-finai,” in ji shi.

Ya ce ya riga ya fara gayyatar jaruman kudu kamar Kanayo O. Kanayo don yin aiki tare da su.

“Burin da nake da shi ga wannan masana’anta ba zai mutu ba. In Allah ya bani dama, zan sa Kannywood ta shiga duniya har kowa ya santa.”

Fim ba karamin abu ba ne

Ya ci gaba da cewa harkar fim na dauke da arziki, daukaka, da soyayya daga al’umma.

“Fim na baka suna fiye da yadda kake zato. Wani lokaci ka isa wurare da ko a mafarki ba ka taba tunanin ka isa ba. Gwamna na iya tunanin an san shi a ko’ina, amma haka dan fim ma yake. A karshe dai fim na daga cikin hanyoyin da ke gina mutum.”

Kira ga mutane

A karshe, Maishadda ya shawarci mutane da su daina raina wani, musamman a lokacin da bai kai ko’ina ba.

“A lokacin da na fara wannan sana’a, mutane da dama sun raina ni, sun toshe hanyoyi. Amma yau gashi Allah ya daukaka ni. Abin da ka raina yau, ka iya girmama shi gobe,” in ji Maishadda wanda ake wa lakabi da ‘King of Box Office’ a Kannywood.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks