Nishadi

Masarautar Rano A Kano Ta Haramta Aurar Da Yara Kafin Su Kammala Firamare

Masarautar Rano a jihar Kano ta fitar da sabuwar doka da ta haramta cire yarinya daga makaranta domin aurar da ita kafin ta kammala karatun firamare.

Wannan sanarwa ta fito ne daga sakataren yada labaran masarautar, Nasiru Habu Faragai, wanda ya aike da ita ga manema labarai a ranar Jumu’a.

A cewarsa, Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umaru, ya bayyana wannan mataki a ranar Alhamis, yayin bikin kaddamar da sabon shirin ɗaukar daliban aji ɗaya na shekarar 2025/2026. Shirin ya samu haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta Jiha (SUBEB), UBEC da kuma UNICEF, a garin Lausu da ke masarautar Rano.

Sanarwar ta ce Sarkin ya umarci dagatai, masu unguwanni, sarakunan Fulani da malamai da su tabbatar da bin wannan doka. Ya kuma gargadi cewa duk wanda ya saba mata, za a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.

See also  "Na rage ƙiba ne domin lafiyar kaina, kuma ni a yanzu nafi jin daɗin rayuwa ta, lokacin da nake da ƙiba bana jin daɗin jikina ~ Cewar Jaruma Hadiza Gabon

Haka kuma, Sarkin ya yi kira ga iyaye da malamai da su guji hada baki wajen cire yarinya daga makaranta saboda aure. Ya bayyana cewa wannan dabi’a na iya hana ci gaban rayuwar yara, musamman mata.

A ƙarshe, Sarkin ya bukaci iyaye da shugabannin al’umma da su ba da haɗin kai da goyon bayan da ake buƙata domin ganin gwamnati ta cimma burinta na inganta ilimi a jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks