• Latest
  • Trending
  • All
Masauratar Gidan Igwai Sokoto ta dakatar da kuma tuɓe Soja Boy daka sarautar Yarimar Igwai

Masauratar Gidan Igwai Sokoto ta dakatar da kuma tuɓe Soja Boy daka sarautar Yarimar Igwai

February 4, 2025
Gwamnatin Jihar Niger Ta Daura wa Makarantar St. Mary Alhakin Sace Dalibai

Gwamnatin Jihar Niger Ta Daura wa Makarantar St. Mary Alhakin Sace Dalibai

November 21, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Makarantar Kwana a Jihar Niger, Sun Sace Dalibai

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Makarantar Kwana a Jihar Niger, Sun Sace Dalibai

November 21, 2025
Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Daurin Rai Da Rai

Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Daurin Rai Da Rai

November 21, 2025
Nnamdi Kanu Ya Amince Zai Tuntubi Lauyoyinsa Kafin Ya Fara Kare Kansa

Kotun Tarayya Ta Ci Gaba da Shari’ar Nnamdi Kanu Ba Tare da Shi Ba Bayan Zargin Rashin Ladabi

November 20, 2025
ASUU Benin Ta Karyata Sabon Ƙarin Albashi: “Ba Zai Hana Ƙaurawar Malamai Ba

ASUU Benin Ta Karyata Sabon Ƙarin Albashi: “Ba Zai Hana Ƙaurawar Malamai Ba

November 20, 2025
NELFUND Za Ta Fadada Lamunin Dalibai Zuwa Sana’o’i da Fasaha a Najeriya

NELFUND Za Ta Fadada Lamunin Dalibai Zuwa Sana’o’i da Fasaha a Najeriya

November 17, 2025
Willie Obiano Yana Raye Cikin Koshin Lafiya a Amurka – An Karyata Jita-Jitar Mutuwarsa

Willie Obiano Yana Raye Cikin Koshin Lafiya a Amurka – An Karyata Jita-Jitar Mutuwarsa

November 15, 2025
Najeriya 4–1 Gabon: Super Eagles Sun Tsallake Zuwa Wasan Karshe

Najeriya 4–1 Gabon: Super Eagles Sun Tsallake Zuwa Wasan Karshe

November 13, 2025
Ba zan bari a gina filin da ba shi da takardu ba – Ministan Abuja Wike

Ba zan bari a gina filin da ba shi da takardu ba – Ministan Abuja Wike

November 12, 2025
Matsalar Tsaro a Kano: 'Yan sa kai na ƙauyen Shanono suna sintiri domin kare al’umma daga harin ƴan bindiga.

Matsalar Tsaro a Kano: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Faruruwa, Sun Yi Garkuwa da Mata Biyar

November 12, 2025
NYSC Ta Fitar da Lambobin Kira Ga Mambobin Batch C Na 2025

NYSC Ta Fitar da Lambobin Kira Ga Mambobin Batch C Na 2025

November 11, 2025
Rikicin Nyesom Wike da Sojojin Najeriya: Abin da ya faru a Abuja

Rikicin Nyesom Wike da Sojojin Najeriya: Abin da ya faru a Abuja

November 11, 2025
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood
Tuesday, December 2, 2025
NgHausa News
  • Login
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood
No Result
View All Result
NgHausa News
No Result
View All Result
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood
🚀 Join Our Telegram Community

Masauratar Gidan Igwai Sokoto ta dakatar da kuma tuɓe Soja Boy daka sarautar Yarimar Igwai

by NgHausa
February 4, 2025
in Labaran Duniya
0
Masauratar Gidan Igwai Sokoto ta dakatar da kuma tuɓe Soja Boy daka sarautar Yarimar Igwai
0
SHARES
567
VIEWS

MASARAUTAR GIDAN AGWAI DA KE JIHAR SOKOTO TA TUƁE MAWAƘI USMAN UMAR (SOJABOY) DAGA SARAUTAR YARIMAN GIDAN AGWAI

Masarautar Gidan Agwai ta bayyana tuɓe mawaƙi Usman Umar, wanda aka fi sani da Sojaboy, daga sarautar Yariman Gidan Agwai.

Idan za a tuna, mujallar Fim ta ruwaito cewa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta dakatar da Sojaboy daga shiga harkokin Kannywood sakamakon wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda aka ganshi yana rungumar wasu mata.

A wata takarda da masarautar ta aika masa, ɗauke da sa-hannun Alhaji Abubakar Marafa a madadin Sarkin Adar Gidan Agwai, an bayyana cewa:

“An umarce ni a madadin mai girma Marafan Gidan Agwai domin gabatar da wannan takarda ta dakatarwa da kuma tuɓewar ka daga sarautar Yariman Gidan Agwai saboda yaɗa bidiyo mai ɗauke da shagala, rafkana da badala, wanda ya saɓa wa addini, al’ada da ɗabi’un unguwar Gidan Agwai da al’ummar da ke cikinta.

“Gundumar Gidan Agwai da ɗaukacin al’ummarta sun yi tir da wannan lamari, kuma sun barranta da kansu daga wannan mummunar dabi’a da rashin dattako.

“Muna addu’a da fatar za ka gyara halayenka, ka kuma saita rayuwarka bisa tarbiyya, addini da ɗabi’unmu na Musulunci. Wassalam.”

A takardar, an nuna cewa an aika da kwafenta ga fadar Sarkin Musulmi, da ofisoshin Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato, da Kwamishinan ’Yan sanda, da Daraktan DSS, da Civil Defence na jihar, da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Sokoto ta Arewa.

See also  Naira Ta Kara Dorewa: Dala Ta Karkata Tsakanin ₦1,437 Zuwa ₦1,455 a Kasuwar Musayar Kudi

A yayin da Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yanke hukuncin dakatar da Sojaboy daga Kannywood, ta kuma haɗa da jaruman matan da suka bayyana a bidiyon, wato Shamsiyya Muhammad da Hasina Suzan.

Hukumar ta yanke wannan hukunci ne bayan bayyanar wasu bidiyoyi daga sabuwar waƙarsa mai suna Bugun Zuciya, wacce ta nuna abubuwan da suka saɓa wa addini, al’ada, ƙa’idoji da ɗabi’un jihar Kano.

A cewar hukumar, ta samu ƙorafe-ƙorafe daga al’umma da malamai game da wannan batu.

A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa-hannun jami’in yaɗa labaran hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, an bayyana cewa an sha gargaɗin Sojaboy kan ire-iren waɗannan abubuwa da suka shafi lalata da rashin mutunci.

See also  Mummunan Hari Kan Masallatai: Kalubale Ga Tsaro a Najeriya

Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya umurci sashen tacewa da su tabbatar da cewa Sojaboy da jaruman mata biyun ba su shiga cikin duk wani shiri na Kannywood ba. Haka kuma, ya umarci duk wuraren shirya finafinai da nishaɗi da su kula da wannan mataki.

Share this:

  • Click to share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Click to share on X (Opens in new window) X
Join our WhatsApp Channel
NgHausa

NgHausa

Related Posts

Gwamnatin Jihar Niger Ta Daura wa Makarantar St. Mary Alhakin Sace Dalibai

Gwamnatin Jihar Niger Ta Daura wa Makarantar St. Mary Alhakin Sace Dalibai

by NgHausa
November 21, 2025
0

Gwamnatin jihar Niger ta dora wa makarantar St. Mary alhakin sace ɗaliban da ƴan bindiga suka yi a tsakar daren...

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Makarantar Kwana a Jihar Niger, Sun Sace Dalibai

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Makarantar Kwana a Jihar Niger, Sun Sace Dalibai

by NgHausa
November 21, 2025
0

Gwamnatin jihar Niger da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta tabbatar da aukuwar wani hari da Yan bindiga suka kai...

Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Daurin Rai Da Rai

Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Daurin Rai Da Rai

by NgHausa
November 21, 2025
0

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, hukuncin daurin rai da rai bayan...

Nnamdi Kanu Ya Amince Zai Tuntubi Lauyoyinsa Kafin Ya Fara Kare Kansa

Kotun Tarayya Ta Ci Gaba da Shari’ar Nnamdi Kanu Ba Tare da Shi Ba Bayan Zargin Rashin Ladabi

by NgHausa
November 20, 2025
0

Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya fara karanta hukunci a shari’ar ta’addanci da aka...

Recent Posts

  • Gwamnatin Jihar Niger Ta Daura wa Makarantar St. Mary Alhakin Sace Dalibai
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Makarantar Kwana a Jihar Niger, Sun Sace Dalibai
  • Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Daurin Rai Da Rai
  • Kotun Tarayya Ta Ci Gaba da Shari’ar Nnamdi Kanu Ba Tare da Shi Ba Bayan Zargin Rashin Ladabi
  • ASUU Benin Ta Karyata Sabon Ƙarin Albashi: “Ba Zai Hana Ƙaurawar Malamai Ba

Recent Comments

  1. Yusuf tanko on Brief history of Fatima Hussaini Abbas “Maryam Labarina”
  2. Abdulazeez jibrin on Yadda Zaka Samu Tallafin Kudi a Najeriya (2025): Matakai da Sharuɗɗa
  3. Bashir Gamzaki on COMPLETE RAMADAN TAFSEER 1446/2025 PROF. Isah Ali Ibrahim Pantami
  4. IBB on Brief history of Fatima Hussaini Abbas “Maryam Labarina”
  5. IBB on Brief history of Fatima Hussaini Abbas “Maryam Labarina”

Archives

  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • June 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • February 2025
  • January 2025
  • December 2024
  • November 2024
  • October 2024
  • September 2024
  • August 2024
  • July 2024
  • June 2024

Categories

  • Blog
  • Entertainment
  • Hausa Series
  • KannyWood
  • Labaran Duniya
  • Lafiya
  • Nigeria
  • Nishadi
  • Opportunity
  • Siyasa
  • Sports
  • TAFSEER
  • Wasanni
NgHausa News

© NG Hausa News – 2025

Navigate Site

  • About Us
  • Privacy Policy
  • Terms and Conditions
  • Disclaimer
  • Contact Us

Follow Us

No Result
View All Result
  • Labaran Duniya
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Nishadi
  • KannyWood

© NG Hausa News – 2025

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
Enable Notifications OK No thanks