Masauratar Gidan Igwai Sokoto ta dakatar da kuma tuɓe Soja Boy daka sarautar Yarimar Igwai

MASARAUTAR GIDAN AGWAI DA KE JIHAR SOKOTO TA TUƁE MAWAƘI USMAN UMAR (SOJABOY) DAGA SARAUTAR YARIMAN GIDAN AGWAI
Masarautar Gidan Agwai ta bayyana tuɓe mawaƙi Usman Umar, wanda aka fi sani da Sojaboy, daga sarautar Yariman Gidan Agwai.
Idan za a tuna, mujallar Fim ta ruwaito cewa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta dakatar da Sojaboy daga shiga harkokin Kannywood sakamakon wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, inda aka ganshi yana rungumar wasu mata.
A wata takarda da masarautar ta aika masa, ɗauke da sa-hannun Alhaji Abubakar Marafa a madadin Sarkin Adar Gidan Agwai, an bayyana cewa:
“An umarce ni a madadin mai girma Marafan Gidan Agwai domin gabatar da wannan takarda ta dakatarwa da kuma tuɓewar ka daga sarautar Yariman Gidan Agwai saboda yaɗa bidiyo mai ɗauke da shagala, rafkana da badala, wanda ya saɓa wa addini, al’ada da ɗabi’un unguwar Gidan Agwai da al’ummar da ke cikinta.
“Gundumar Gidan Agwai da ɗaukacin al’ummarta sun yi tir da wannan lamari, kuma sun barranta da kansu daga wannan mummunar dabi’a da rashin dattako.
“Muna addu’a da fatar za ka gyara halayenka, ka kuma saita rayuwarka bisa tarbiyya, addini da ɗabi’unmu na Musulunci. Wassalam.”
A takardar, an nuna cewa an aika da kwafenta ga fadar Sarkin Musulmi, da ofisoshin Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato, da Kwamishinan ’Yan sanda, da Daraktan DSS, da Civil Defence na jihar, da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Sokoto ta Arewa.
A yayin da Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yanke hukuncin dakatar da Sojaboy daga Kannywood, ta kuma haɗa da jaruman matan da suka bayyana a bidiyon, wato Shamsiyya Muhammad da Hasina Suzan.
Hukumar ta yanke wannan hukunci ne bayan bayyanar wasu bidiyoyi daga sabuwar waƙarsa mai suna Bugun Zuciya, wacce ta nuna abubuwan da suka saɓa wa addini, al’ada, ƙa’idoji da ɗabi’un jihar Kano.
A cewar hukumar, ta samu ƙorafe-ƙorafe daga al’umma da malamai game da wannan batu.
A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa-hannun jami’in yaɗa labaran hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, an bayyana cewa an sha gargaɗin Sojaboy kan ire-iren waɗannan abubuwa da suka shafi lalata da rashin mutunci.
Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya umurci sashen tacewa da su tabbatar da cewa Sojaboy da jaruman mata biyun ba su shiga cikin duk wani shiri na Kannywood ba. Haka kuma, ya umarci duk wuraren shirya finafinai da nishaɗi da su kula da wannan mataki.