Matashi Ya Bukaci Rahama Sadau Ta Fito Takarar Shugaban Kasa a 2027

KADUNA – Soshiyal midiya ta dauki zafi bayan wani matashi ya nemi fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta fito takarar shugabar Najeriya a 2027. Kiran ya zo ne bayan Rahama ta wallafa wani sako a shafinta na Facebook wanda ya jawo martanin sama da mutane 2,200.
A cikin sallamar da ta yi, Rahama ta rubuta:
“Salaam…👀”
Haruffa shida da alamomin rubutu uku da alamar ido da jarumar ta rubuta sun yi tasiri a zukatan masoyanta, har aka tafka muhawara kan yiwuwarta ta fito takarar shugaban kasa.
Ana So Rahama Ta Fito Takarar Shugaban Kasa
Daga cikin wadanda suka yi martani, Hamza M Kankia, dan asalin jihar Katsina, ya nemi Rahama ta fito takarar shugaban kasa saboda shahararta da tarin masoyan da take da su. Ya ce:
“Kina da tarin masoya, kawai ki fito takarar shugabar kasar Najeriya.”
Rahama ta sanya alamun ‘aljanun dariya’ a martaninta, yayin da wani Ishaq Babangida Abubakar ya ce:
“Za mu zabe ki, sosai, kina da kirki Rahama.”
Sai dai Kabiru AG ya yi wa Hamza M Kankia martani da cewa lallai Rahama za ta lashe zaben idan na soshiyal midiya ne, “musamman ma ace da Ado Gwanja za ta yi takara.”
Martanin Masu Soshiyal Midiya
Sallamar Rahama ta jawo martanin dubunnan mutane, inda wasu suka yi ta barkwanci da kuma nuna goyon baya. Ga wasu daga cikin martanin:
- Maryam Ameenu:
“Kam bala’i in miniti 3 kin samu sama da martani 400. Sannu kin ji Rahama Sadau ‘yar sababi ❤️😅”
- Abdulsalam Umar:
“A ba mu kudi hajiya 🤗🚶🏿”- Abdullahi Sabo Kibiya:
“Wa’alaikum Salam, gaskiya ina sonki sosai Rahmam. Ina son ki kamar na mutu.”- Fatema Muhammad:
“Ni har yanzu mutane mamaki suke bani, sai kace ba sune shekarun baya suke zagi da nuna kiyayya ga Rahama Sadau ba, amma yanzu su ne ke bibiyarta. Lalle Tinubu ka yi aiki.”- Rabiu Salafii:
“Ya hallata idan Rahama Sadau ta bani kudi na yi anfani dasu? Tambaya nake?”
Bayanin Rahama Sadau
Rahama Sadau ta shahara a masana’antar fina-finai ta Kannywood kuma ta samu mukami a kwamitin shirin saka hannun jari na kere-kere na kasa, wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya nada ta.
Za a iya ci gaba da bin labarin kan yadda muhawarar ke tafko a soshiyal midiya.