Labaran Duniya

Mummunan Hari Kan Masallatai: Kalubale Ga Tsaro a Najeriya

Harin Katsina – 2025

Mummunan harin da ’yan bindiga suka kai a masallacin Unguwar Mantau, Malumfashi (Katsina), ya sake tayar da hankula a Najeriya.

Maharan sun afka wa masallatan ne a lokacin da ake tsaka da sallar asuba, inda suka bude wuta kan masu ibada.

Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 28 tare da jikkatar da wasu da dama. Shaidu daga garin sun tabbatar wa BBC Hausa cewa maharan sun ƙona gidaje, tare da kulle wani dattijo a ɗaki suka zuba fetur suka cinna masa wuta.

Wani shaidar ya ce maharan sun kuma sace kusan mutum 100 ciki har da mata da yara.

See also  Dantata Laid To Rest In Madinah, Dangote, Others Bid Farewell

Hari a Tsafe, Zamfara – 2024

A watan Fabrairu 2024, wasu ’yan bindiga dauke da makamai a kan babura sun kai farmaki masallacin garin Tsafe, Zamfara. An sace kimanin masallata 30 yayin da ake sallar asuba.

Gwamnatin jihar ta sanar da tura jami’an tsaro cikin daji domin ceto wadanda aka sace, abin da ya jawo hankalin kafafen yaɗa labarai a lokacin.

Birnin Gwari, Kaduna – 2023

Rahoton Beacon Security ya nuna cewa a 2023, ’yan bindiga sun kai hari a masallacin Birnin Gwari, inda suka kashe limamin masallacin tare da wasu mutum biyu. Haka kuma wasu biyu sun jikkata yayin da ake sallar asuba.

Bukkuyum, Zamfara – 2022

A shekarar 2022, an samu hari a ƙauyen Ruwan Jema, Bukkuyum (Zamfara). ’Yan bindiga sun kashe mutum 18 a masallacin Juma’a. Shaidu sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na rana a lokacin da ake shirin sallar Juma’a.

See also  Hukumar tace fina-finai ta haramta bikin 'ƙauyawa' a jihar Kano

Maigamji, Katsina – 2022

A watan Disamba 2022, wasu ’yan bindiga sun kai hari masallacin Maigamji (Funtua, Katsina) inda suka sace kusan mutum 20 a yayin sallar Isha’i. Limamin masallacin da wani mutum sun jikkata, amma daga baya aka sallame su daga asibiti.

Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da ceto wasu daga cikin wadanda aka sace tare da taimakon jami’an tsaro da ’yan sa kai.

Jibia, Katsina – 2021

A shekarar 2021, ’yan bindiga sun kai hari masallacin Abbatuwa, Jibia (Katsina). Sun sace akalla mutum 40 yayin sallar Tahajjud, duk da cewa daga baya mutum 30 sun kuɓuta.
Maharan sun zagaye masallacin, suka lalata na’urar amo, sannan suka tilasta wa jama’a fita waje kafin su yi awon gaba da mutanen.

Me yasa ’Yan Bindiga Ke Kai Hari Masallatai?

Mummunan hari Jama’a suna gudanar da jana’izar mutanen da suka rasu a Unguwar Mantau, Katsina

Dakta Kabiru Adamu, shugaban Beacon Security, ya ce maharan na kai farmaki a masallatai ne domin:

  • Nuna iko da razana jama’a
  • Samun damar sace mutane masu yawa lokaci guda saboda masallaci wurin taruwar jama’a ne.
  • Rashin tsaro a masallatai, domin ba a ajiye makamai a ciki.
See also  Dalar Amurka Ta Fadi: Me Wannan Ke Nufi?

Ya ce maharan kuma na amfani da hare-haren domin ɗaukar hankalin duniya kan ayyukansu.

Yadda Za a Kare Masallatai

Dakta Kabiru Adamu ya ba da shawarwari kan kariya:

  1. Inganta tsaro a masallatai – gwamnati ta ɗauki nauyi, amma idan ba ta yi ba, sai al’umma su haɗu.
  2. Tsarin addini – a raba jama’a gida biyu: rukunin farko ya yi sallah, na biyu ya tsare, sannan su musanya.
  3. Ƙarin jami’an tsaro – gwamnati ta tsananta tsaro musamman a wuraren ibada.
  4. Faɗakarwa daga malamai – a koyar da muhimmancin masallatai da kuma illar kai musu hari.

Hare-hare kan masallatai sun zama babban barazana ga tsaro da rayuwar al’umma a Najeriya.

Duk da matakan da gwamnati da jami’an tsaro ke ɗauka, sake faruwar irin wadannan hare-hare na nuna cewa akwai buƙatar ƙarin tsari, haɗin kai da faɗakarwa domin kare wuraren ibada da al’umma gaba ɗaya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks