Nishadi

Murja Kunya: Ko dai Alkali Zaria ya Aure Ni Ko in shiga duniya on koma Lagos

Fitacciyar ɗiyar soshiyal midiya, Murja Kunya, ta sake janyo hankalin jama’a da wani sabon bayani da ta yi a TikTok.

A cikin saƙon nata, Murja ta bayyana cewa tana da burin zama matar shahararren malamin Musulunci, Alƙali Salihu Zaria.

Ta ce abin da ya fi janyo hankalinta game da Alƙali Zaria shi ne halinsa na fadin gaskiya ba tare da jin tsoro ba, komai raɗaɗin gaskiyar.

Murja Kunya ta ƙara da cewa irin wannan halayya ce take burgeta, saboda tana ganin irin mutane masu gaskiya sun ragu a wannan zamanin.

A cikin wani salon barkwanci, ta ce: “Ko dai Alƙali Zaria ya aure ni, ko kuma in bar wannan duniya in koma Legas!”

Wannan furuci ya tayar da kura sosai a soshiyal midiya, inda masoya da masu bibiyarta ke tofa albarkacin bakinsu.

@murjakunya0

🤸‍♂️🤸‍♂️🤸‍♂️💃💃💃🕺🩸

♬ original sound – YAGAMEN

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button