Nishadi
“Na rage ƙiba ne domin lafiyar kaina, kuma ni a yanzu nafi jin daɗin rayuwa ta, lokacin da nake da ƙiba bana jin daɗin jikina ~ Cewar Jaruma Hadiza Gabon

Jaruma Hadiza Gabon ta bayyana cewa ta rage ƙiba ne domin lafiyar kanta. Ta ce lafiya ita ce tafi kowanne abu muhimmanci a rayuwa.
Ta bayyana cewa kafin ta rage kiba, ba ta jin daɗin jikinta. Duk da cewa tana rayuwa, amma akwai abubuwan da ke hana ta jin kwanciyar hankali da sauƙin motsi.
Yanzu da ta rage ƙiba, tana jin daɗin rayuwarta fiye da da. Ta ce jikinta ya fi sauƙi, kuma tana iya gudanar da ayyukanta cikin sauƙi da ƙarfi.
A ƙarshe, ta bukaci mata da su mayar da hankali kan lafiyarsu. Ta ce rage ƙiba ba wai don kwalliya kawai ba, illa don jin daɗin rayuwa da kariya daga cututtuka.