Nigeria

Janar Christopher Musa ya shawarci ’yan Najeriya su koyi dabarun kare kai

Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya shawarci ’yan ƙasa da su koyi dabarun kare kai daga haɗurra, a matsayin mataki na ko-ta-kwana don tsare rayuwarsu.

Janar Christopher Musa ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels TV a ranar Alhamis.

A cewarsa, matsalolin tsaro na ci gaba da addabar sassan ƙasar, musamman a arewa maso yamma, arewa maso gabas, da kuma arewa ta tsakiya, inda ’yan bindiga ke kashe mutane tare da raba su da muhallansu. Duk da cewa hukumomi na cewa suna ƙoƙari wajen magance lamarin, amma har yanzu daruruwan mutane na ci gaba da rasa rayukansu.

See also  Gwamnatin Katsina Ta Ce Tallafin Da Ta Baiwa Yan Bindiga Da Suka Tuba Zai Rage Matsalar Tsaro

Lokacin da aka tambaye shi ko ya dace al’umma su koyi dabarun faɗa, sai ya ce:

“Ya kamata mutane su ɗauki kare kai a matsayin ilimin da ake buƙata a rayuwa, kamar koyon tuƙi ko kuma iyo. Wannan muhimmin abu ne, ko da a lokacin zaman lafiya ko kuma lokacin yaƙi.”

Janar Musa ya ƙara da cewa wajibi ne a wayar da kan kowane ɗan Najeriya kan tsaro a kowane mataki, domin kare kai na da matuƙar muhimmanci ga rayuwa.

A matsayin misali, a ranar Litinin da ta gabata, wasu ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 28 a lokacin sallar asuba a wani masallaci da ke ƙaramar hukumar Malumfashi, Jihar Katsina.

See also  Dalilai uku da suka sa ɗaliban Kano suka yi zarra a jarrabawar NECO ta 2025

Haka kuma, a watan da ya gabata, masu garkuwa da mutane sun yi wa mutum 38 yankan rago daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara, lamarin da ya sake tayar da hankula a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks