Labaran Duniya

Nigeria ta kori ’yan ƙasashen waje 102 kan laifin damfara ta intanet

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta mayar da ’yan ƙasashen waje 102 gida, bayan kama su da laifin damfara ta intanet. Daga cikin waɗanda aka kora, akwai ’yan China 60 da ’yan ƙasar Philippines 39.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar (EFCC) ce ta fitar da sanarwar a yau Alhamis.

Tun farko EFCC ta sanar da kora ’yan China 50, amma daga baya kakakin hukumar, Dele Oyewale, ya ce an ƙara korar wasu ’yan China 10 da kuma mutane biyu ’yan ƙasar Kazakhstan, tun daga ranar 15 ga watan Agusta.

Ya kuma bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da korar bakin da aka kama da irin waɗannan laifuka a kwanaki masu zuwa.

See also  I will not be concerned if another governor tries to remove me - Emir of Kano Sanusi II

Waɗannan mutane sun fito daga cikin mutum 792 da aka kama a Legas a watan Disambar bara bisa zargin damfara ta intanet. A cikinsu kuwa, 192 ’yan ƙasashen waje ne, ciki har da ’yan China 148.

Najeriya dai ta shahara a duniya da matsalar damfara ta intanet, wadda ake kira “Yahoo-Yahoo”, matsalar da ta yi ta ci gaba da bazuwa duk da ƙoƙarin hukumomi na dakile ta.

A baya-bayan nan, EFCC ta ce ta bankaɗo wasu cibiyoyin koyar da matasa dabarun damfara ta intanet, lamarin da ya ƙara jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks