Isra’ila Ta Kai Hari Kan Sansanonin Houthi a Sana’a da Al-Jawf

Rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin mayaƙan Houthi a Sana’a, babban birnin Yemen, da kuma yankin Al-Jawf.
An ce an lalata sansanonin soja, shalkwatar abin da Isra’ila ta kira sashen yaɗa farfaganda na Houthi, da kuma rumbunan ajiyar man fetur.
Sai dai Ma’aikatar Lafiyar Houthi ta tabbatar da cewa akalla mutum 35 sun mutu, yayin da fiye da 130 suka jikkata.
Bidiyoyin da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna mummunar fashewa a Sana’a sakamakon hare-haren.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan mayaƙan Houthi sun harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuƙa kan Isra’ila.
A watan da ya gabata ma, Isra’ila ta kai hari sama kan manyan jagororin Houthi, inda ta kashe wasu daga cikinsu, ciki har da wanda ya ayyana kansa a matsayin firaministan gwamnatin ƙungiyar.