Labaran Duniya

Rashin Wuta: Najeriya Ta Fuskanci Faɗuwar Wutar Lantarki Zuwa 1.5 Megawatts

Rashin Wutar Lantarki Ya Shafi Najeriya

A safiyar Laraba, ƙarfin wutar lantarki a Najeriya ya faɗi daga 2,917.83 megawatts zuwa 1.5 megawatts kacal tsakanin ƙarfe 11:00 da 12:00 na rana.

Shafin babban layin wutar lantarki na ƙasa a X ya bayyana cewa an samu matsala mai tsanani, amma an fara aiki don shawo kanta.

Bincike ya nuna cewa kusan dukkanin tashoshin samar da wuta sun tsaya cak, sai na Ibadan kaɗai da ya ci gaba da aiki.

A Abuja, kamfanin rarraba wutar lantarki (Abuja Disco) ya tabbatar wa da abokan hulɗarsa cewa matsalar ba daga hannunsu take ba, illa ta samo asali ne daga babban layin ƙasa.

“Ya ku abokan hulɗarmu, muna sanar da ku cewa rashin wutar da ake fuskanta ya samo asali ne daga babban layin wutar ƙasa tun daga ƙarfe 11:23 na safiyar yau,” in ji sanarwar Abuja Disco.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks