Wasanni

Real Madrid Ta Doke Real Sociedad 2-1, Ta Ci Nasara a Duk Wasanni Huɗu na Farko

Real Madrid ta ci gaba da jan ragamar Gasar La Liga bayan da ta doke Real Sociedad da ci 2-1 a wasan mako na huɗu da aka buga ranar Asabar.

Kylian Mbappé ne ya fara jefa kwallo ta farko ga Los Blancos, kafin Arda Güler ya ƙara na biyu. Real Sociedad ta dawo cikin wasan ne ta hannun Mikel Oyarzabal wanda ya zura kwallo daga bugun fenariti.

Real Madrid ta ci gaba da buga wasan da ƴan wasa 10 tun daga minti na 32 bayan Dean Huijsen ya samu jan kati, duk da haka ta iya kare nasarar.

Wannan sakamako ya tabbatar da cewa Real Madrid ta lashe dukkan wasanninta huɗu na farko a wannan kakar La Liga.

See also  PSG ta Zazzga wa REAL MADRID 4-0

A mako mai zuwa, Real Madrid za ta karɓi bakuncin Marseille a wasan farko na rukuni a gasar Champions League, sannan ta fuskanci Espanyol a Santiago Bernabéu a gasar La Liga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks