Abuja – Fitacciyar jarumar Nollywood, Regina Daniels, ta zargi mijinta, Sanata Ned Nwoko, da bayar da umarnin kama babban ɗan uwanta da babbar ‘yar uwarta, yayin da ƙanwarta ma ke fuskantar haɗarin kamuwa.
Jarumar ta bayyana wannan ne cikin rubuce-rubuce masu taushi da kuka da ta wallafa a shafinta na Instagram, tana cewa ana kai wa iyalinta hari saboda matsalolin da ke faruwa tsakaninta da mijinta.
A cewar Regina, Sanata Nwoko yana amfani da tasirinsa na siyasa domin tsoratar da ‘yan uwanta da kuma raunana su. Sai dai, ta ce ba ta san ainihin inda ake tsare da su ba, ko kuma dalilin kamun ba.
Ta yi nuni da cewa, ana yi ne domin tilasta mata komawa wani shiri na gyaran halayya (rehab) kamar yadda mijinta ya bukata.
Kukan Regina A Instagram
A cikin sakonnin da ta wallafa a shafinta, Regina ta bayyana cikin bacin rai da tashin hankali:
“Allah wani ya taimake ni! Ina ji kamar na haukace.
An kama babban ɗan uwana da babbar ‘yar uwata, kuma ana shirin kama ƙanwata ma har sai na koma — in koma gidan gyara kamar yadda ya ce.Ban taɓa tunanin zan yi haka ba, amma an kama su saboda ni!
Ka ce ni ‘yar miyagun ƙwayoyi ce? Ni? Kai fa, Allah ya isa!Wane irin suna kake son ka kira ni? Karuwa?
Amma wata rana zan faɗi gaskiya, in gaya wa duniya duk abin da ka aikata.Ina ƙoƙari in zama mai haƙuri saboda ba na son magana, amma fa ni ƙarama ce, yarinya ce, ina jin zafi sosai. Don haka zan iya yin kamar ‘yar shekara 24 mai zafin rai in faɗi radadina.”
Dalilin Da Yasa Ta Yi Shiru
Regina Daniels ta ce ta daɗe tana haƙuri da shiru saboda ƙaunar da take yi wa ‘ya’yanta, waɗanda ta bayyana a matsayin “babban kalubale a rayuwarta.”
Ta ce yanzu, halin da ake ciki ya kai matakin da ba za ta iya jurewa ba.
“Ka bar iyalina, Ned! Ka bar ni lafiya ma!
A bayyane yake yanzu cewa wannan lamari ya zama yaƙi.”
Martani A Shafukan Sada Zumunta
Har yanzu Sanata Ned Nwoko bai mayar da martani ba kan waɗannan zarge-zarge.
Sai dai labarin ya jawo gagarumin cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda mutane suka raba ra’ayoyinsu — wasu suna nuna goyon baya ga Regina, yayin da wasu ke kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin.













