Ronaldo Ya Kafa Tarihi, Portugal Ta Doke Jamus a Gasar UEFA Nations League

Ɗan wasan tsakiyar Jamus, Florian Wirtz, ne ya fara jefa kwallo a ragar Portugal, mintuna kaɗan bayan komawa daga hutun rabin lokaci.
Sai dai Portugal ta dawo da ƙarfi a zagaye na biyu. A minti na 63, Francisco Conceição ya farke kwallon. Bayan minti biyar kacal, Cristiano Ronaldo ya ƙara ta biyu, wanda ta tabbatar da nasarar Portugal.
Wannan kwallo ta Ronaldo ita ce ta 137 da ya ci wa ƙasarsa a jimillar wasanni 220, wanda hakan ya ƙara masa tarihi. Haka kuma, yanzu ya zama ɗan wasan da ya fi zura kwallo a kakar guda a gasar UEFA Nations League, inda ya ci kwallo 7 a bana.
Jimillar kwallayen da Ronaldo ya ci a dukkan wasanninsa yanzu sun kai 937 – adadin da babu wani ɗan wasa da ya taɓa kaiwa a tarihi.
A gefe guda, wannan ce nasarar farko da Ronaldo ya samu kan Jamus, domin a baya bai taɓa doke su ba a wasannin da suka fafata.
Portugal, wadda ita ce ta lashe gasar UEFA Nations League a karo na farko a shekarar 2019, yanzu tana jiran ɗaya daga cikin ƙasashen Spain ko Faransa, waɗanda za su fafata a yau domin sanin wanda za su kara da shi a wasan ƙarshe a ranar Lahadi.