Rundunar Ƴan Sanda a Kano Ta Haramta Hawan Sallah Saboda Barazanar Fitina

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta sanar da haramcin gudanar da hawan sallah a lokacin bukukuwan ƙaramar sallah da ke tafe.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke birnin Kano.
“Mun ɗauki wannan mataki ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa wasu mutane da aka ɗauka haya tare da wasu mazauna birnin za su yi yunkurin tayar da tarzoma ta fake da hawan sallah,” in ji Kwamishinan.
Kwamishinan ya ƙara da cewa an yanke wannan shawara ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
Matakin Ya Saɓa da Niyar Gwamnati da Masarauta
Wannan mataki na ƴan sanda ya ci karo da aniyar gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin NNPP, wadda ta bayyana shirin gudanar da hawan sallah tare da dukkan masarautun Kano huɗu ƙarƙashin jagorancin Sarki Muhammadu Sanusi II.
Shi ma Sarki Sanusi ya riga ya aika wasiƙa ga hukumomin tsaro, yana sanar da shirinsa na gudanar da wannan biki na al’ada kamar yadda aka saba duk shekara.
Sai dai zuwa yanzu, gwamnatin Kano da masarautar ba su fitar da wata sanarwa kai tsaye ba dangane da haramcin hawan.
Sarkin Kano na 15 Ya Soke Hawan Sallah
A gefe guda, Aminu Ado Bayero, wanda ke ci gaba da kiran kansa Sarkin Kano duk da sauke shi da gwamnatin jihar ta yi, ya sanar da soke shirin gudanar da hawan sallah.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne bisa shawarar malamai, iyaye da wasu ‘yan majalisa.
“Hawan sallah ba abu ne na ko a mutu ko a yi rai ba. Idan har zai kawo rikici ko tashin hankali, to wajibi ne mu haƙura,” in ji Aminu Ado Bayero.