Labaran Duniya

Sana’ar yankan farce ta kai ni inda ni kaina ina mamaki – Rabi’u

Wani matashi daga jihar Kano, Rabi’u Halliru, ya ba da mamaki a wata sana’ar da da dama ke ɗauka da ƙasƙanci. Duk da kasancewarsa almajiri a jihar Nasarawa, Rabi’u ya ƙi rungumar bara, inda ya nemi mafita ta halaltacciyar hanya.

Ya zaɓi sana’ar yankan farce – amma ba yadda aka saba ba – ya zamanantar da ita ta hanyar shigar asibiti da amfani da kayan aikin likita.

Na zaɓi wannan sana’ar ne saboda ba ta buƙatar kuɗi da yawa. Amma ban so in yi ta irin ta tsofaffi ba, shi ya sa na kawo salo na daban,” in ji Rabiu, wanda ke yawo daga Nasarawa zuwa Abuja don gudanar da sana’ar tasa cikin kwarjini da tsafta.

See also  Rundunar Ƴan Sanda a Kano Ta Haramta Hawan Sallah Saboda Barazanar Fitina

Nasara da Goyon Bayan da Ya Samu

Rayuwar Rabi’u ta canza lokacin da ya yi wa wani tsohon sanata aikin yankan farce a Nasarawa. A cikin jin daɗi da sanata ya samu, ya ɗauki nauyin karatunsa na sakandare.

A wani lokaci kuma, wata mata ta haɗa shi da mijinta wanda ya nema masa aiki a babban asibiti – duk saboda sana’ar sa.

Idan na tuna daga inda na fito, sai kawai na ce Alhamdulillah. Ba zan taɓa mantawa da waɗanda suka taimake ni ba,” in ji Rabi’u cike da godiya da farin ciki.

See also  Za mu ɗauki mataki kan Sheikh Lawan Triumph bayan karɓar ƙorafi a rubuce - Gwamnan Kano

Buri da Dabarar Ci gaba

Matashi Ya Zamantantar da Sana’ar Yankan Farce – Labarin Rabi’u Halliru
Rabi’u Halliru

Yanzu haka, Rabi’u na fatan komawa makaranta domin ya ɗora iliminsa a hukumance. Ya na kallon kayan aikin sa a matsayin matakin shiri kafin ya zama cikakken jami’in lafiya a nan gaba.

Wasu abokaina sun taɓa dariya da shigar da nake yi. Amma ni na san inda nake dosa, kuma nasan ina neman halak,” ya bayyana da ƙwarin guiwa.

A kullum, yana iya samun fiye da ₦10,000 zuwa ₦15,000 a rana – wata shaida cewa babu abin ƙasƙanci cikin sana’ar hannu idan aka ba ta muhimmanci da tsafta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks