Siyasa

Sabon Rikici Ya Kunno Kai a Jam’iyyar SDP Ta Dakatar Da El-Rufai

An samu sabon rikici a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) biyo bayan dakatarwar da wani bangare na jam’iyyar ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

A cewar wani bangare da ke ikirarin shi ne sahihin shugabancin jam’iyyar, El-Rufai an dakatar da shi ne na tsawon shekaru 30, saboda zargin cigaba da bayyana kansa a matsayin ɗan jam’iyyar duk da dakatar da shi tun a baya.

Dalilin Dakatarwar

SDP Ta Dakatar Da El-Rufai, A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mista Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar, SDP ta ce Malam El-Rufai ba ya da hurumin amfani da sunan jam’iyyar ko yin wata alaƙa da ita.

“Mun dakatar da Malam El-Rufai har na tsawon shekaru 30. Hakan na nufin ba zai iya amfani da sunanmu ko alamar jam’iyya ba, ko ya nuna goyon baya ta kowace hanya,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta bayyana cewa ta yanke wannan hukuncin ne bayan wani babban taro, inda ta nuna rashin amincewa da yadda tsohon gwamnan ke cigaba da shiga harkokinta, duk da cewa ya shiga wani haɗin gwiwar siyasa da ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark.

See also  APC 2027: ANPP na neman a bar mata mataimakin shugaban ƙasa

Martanin Magoya Bayan El-Rufai

Kawo yanzu, Malam Nasir El-Rufai bai fitar da wata sanarwa kai tsaye ba game da wannan dakatarwa. Sai dai, wani na hannun damarsa a jam’iyyar, Hon. Abdullahi Mai Kano, ya bayyana cewa matakin ba shi da tushe a tsarin mulkin jam’iyyar. SDP Ta Dakatar Da El-Rufai

“Wannan dakatarwar babu shi a cikin kundin tsarin SDP. Saboda haka matakin bai da inganci,” in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa El-Rufai na da cikakken katin zama ɗan jam’iyyar SDP, kuma sunansa yana cikin sabbin rajista na jam’iyyar a mazaɓarsa ta Unguwar Sarki, Kaduna.

Kan Zargin Wargaza Jam’iyyar

Dangane da zargin cewa El-Rufai yana shirin karya jam’iyyar SDP ta hanyar haɗa kanta da ADC, Hon. Abdullahi ya musanta hakan.

“Malam Nasir ya shigo SDP ne da niyyar gyara, ba tare da wata mugun nufi ba. Amma wasu na jam’iyyar suna fassara hakan da akasin haka,” in ji shi.

Ra’ayin Masani

A nasa bangaren, Farfesa Abubakar Kari daga Jami’ar Abuja ya bayyana cewa irin wannan ce-ce-ku-ce ba sabo ba ne a siyasar Najeriya.

“A mafi yawan jam’iyyun Najeriya, akwai mutane masu faɗa aji da ke yanke hukunci ba tare da bin ka’idojin dimokuraɗiyya ba. Wannan matsala ce da ke hana jam’iyyun ci gaba da zama tsayayyu,” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks