Labaran Duniya

Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Kan Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana marigayi Muhammadu Buhari a matsayin “ɗan kishin ƙasa na gaskiya, soja jajirtacce, kuma dattijo wanda ba za a taɓa mantawa da sadaukarwar da ya yi wa ƙasar nan ba.”

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a yau Lahadi, Tinubu ya ce ya ji matuƙar ɓacin rai da kaduwa da rasuwar tsohon shugaban. Ya ƙara da cewa Buhari zai ci gaba da kasancewa abin tunawa saboda jajircewarsa wajen hidimar ƙasa, ƙoƙarinsa na haɗin kai, da kuma sadaukarwarsa wajen cigaban Najeriya.

Marigayi Muhammadu Buhari ya rasu ne a yau Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan, yana da shekara 82. Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa ya rasu bayan doguwar jinya.

See also  Sana'ar yankan farce ta kai ni inda ni kaina ina mamaki - Rabi'u

A cewar sanarwar, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranci dawowar gawar Buhari daga Landan zuwa Najeriya domin gudanar da jana’iza.

A cikin wannan rana, Shugaba Tinubu ya jagoranci wani taron gaggawa na majalisar zartarwa domin girmama tsohon shugaban ƙasa da ya rasu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks