Labaran Duniya

Damfara ta Internet: Hanyoyin da ake amfani da su da yadda za ka kare kanka

Intanet da Matsalar Damfara

A yau, intanet ta zama hanya mafi sauƙi wajen sadarwa, kasuwanci, da samun bayanai. Amma kamar yadda take da amfani, haka kuma ta zama cibiyar damfara.


Masu damfara suna amfani da dabaru iri-iri domin yaudarar mutane, su sace musu kuɗi ko bayanai masu muhimmanci. Wannan matsala ta shafi kowa – matasa da manya – musamman a ƙasashe masu tasowa irin su Najeriya. Rahotanni sun nuna dubban mutane na rasa miliyoyi saboda damfara ta intanet.

Yadda Masu Damfara ke Aiki

Abdullahi Salihu Abubakar, masani kan kafofin sada zumunta, ya ce masu damfara ba sa amfani da intanet kaɗai. Suna da dabaru daban-daban, ciki har da:

  • Nazarin halaye – suna duba abin da mutum yake so kafin su aika saƙo.
  • Lura da ɗabi’u – suna fahimtar yadda mutum ke mu’amala domin su ja hankalinsa.
  • Tsara dabaru – suna ƙirƙirar labarai ko saƙonni da za su sa mutum ya yarda da su.
  • Aika saƙon karya – suna iya kiran mutum daga lamba da ba a sani ba, suna cewa bankinsa na da matsala.
  • Amfani da shafukan boge – suna ƙirƙirar shafin da ya yi kama da na gaskiya, misali na banki, domin su sace bayanai.
  • Social engineering – suna nuna kamar sun san mutum, ta WhatsApp, Facebook, ko imel.
  • Tallace-tallace na ƙarya – sukan ce za a samu aiki, rance, ko kuɗi cikin sauƙi.
See also  Ƴanta'adda sun kashe mutum 127 a hare-hare biyar a Nijar - HRW

Mummunan Tasirin Damfara

Duk wanda ya faɗa tarkon masu damfara kan gamu da matsaloli da dama:

  • Ƙuncin rayuwa, damuwa ko ma hauka.
  • Rashin amincewa da saƙonni da mutane.
  • Asarar kuɗi da zuba jari a ayyuka na boge.
  • Tattalin arziki ya ragu saboda mutanen da aka cuta ba sa iya cigaba da harkokinsu.

Hanyoyin Kare Kai Daga Damfara

Masana sun bayar da shawarwari da dama domin kare kai daga zamba ta intanet:

  1. Yi amfani da makulli mai mataki biyu (two-step verification).
    Wannan tsari yana ƙara kariya a asusun banki ko na kafofin sada zumunta.
  2. Koyi amfani da intanet da shafuka cikin tsaro.
    Sanin yadda ake gane saƙonnin boge zai kare mutum daga shiga tarkon damfara.
  3. Sanin Netiquette (ɗabi’un intanet).
    Kada ka buɗe shafin da aka turo maka daga wuri da ba ka sani ba.
  4. Tantance kira daga wanda ba ka sani ba.
    Ka tambayi wanda ya kira sunansa da inda ya samo lambarka.
  5. Guji saƙonnin samun kuɗi cikin sauƙi.
    Duk saƙon da ya yi alkawarin arziki cikin gaggawa yawanci yaudara ne.
  6. Kariya daga shafukan boge (phishing).
    Ka tabbatar adireshin da aka turo maka daga banki ko kamfani na gaskiya ne, ba na boge ba.
See also  Hukumar EFCC reshen Kano ta cafke fitacciyar ƴar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, bisa zargin yin liƙi da kuɗin Najeriya.

Damfara ta internet babbar barazana ce ga jama’a. Amma da ilimi, taka-tsantsan, da bin shawarwarin tsaro, mutum zai iya kaucewa fadawa tarkon masu damfara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks