Dalibin BUK Ya Rasa Ransa Bayan Harin Masu Kwacen Waya a Kano

Umar Abdullahi Hafizi, dalibin buk a shekarar ƙarshe mai karatun Sociology a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), ya rasa ransa sakamakon harin da wasu da ake zargin ‘yan ƙwacen waya ne suka kai masa.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Talata, a unguwar Dorayi da ke Ƙaramar Hukumar Gwale, Jihar Kano.
Yadda Lamarin Ya Faru
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun soka Umar da wuka, sannan suka tsere da wayarsa. Bayan an garzaya da shi asibiti, ya rasu sakamakon munanan raunukan da ya samu.
Martanin Jami’a da Hukumomi
Jami’ar BUK ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai, Malam Lamara Garba, ya fitar. Sanarwar ta nuna jimamin jami’ar tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, abokansa da sauran ɗalibai.
Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin kama masu laifin.
An Yi Jana’iza a Zariya
An binne marigayin a garinsu da ke Zariya, Jihar Kaduna. Jami’ar ta buƙaci ɗalibai da su kwantar da hankalinsu, tare da kasancewa masu lura da lafiyar kansu da muhallinsu.
Haka kuma, an buƙaci jama’a da su taimaka da duk wani bayani da zai iya taimakawa jami’an tsaro wajen gano masu laifin.