UN Ta Zargi Isra’ila da Aikata Kisan Kare Dangi a Gaza

Kwamitin bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ya fitar da sabon rahoto da ya zargi Isra’ila da aikata kisan kare dangi a kan Palasɗinawa a zirin Gaza.
Wannan rahoton ya ƙara hura wutar muhawara da suka da suka daɗe suna tasowa tun bayan fara yaƙin Isra’ila da Hamas a ƙarshen shekarar 2023.
Hujjojin da UN Ta Gabatar
A cewar rahoton, an samu isassun shaida da ke nuna cewa Isra’ila ta aikata huɗu daga cikin abubuwa biyar da ake ɗauka a matsayin ayyukan kisan kare dangi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa. Abubuwan huɗun sun haɗa da:
- Kashe wasu rukunin mutane gaba ɗaya ko a wani ɓangare.
- Jikkata su matuƙa, ciki har da janyo musu matsalolin da suka shafi lafiyar ƙwaƙwalwa da jiki.
- Aikata abubuwa da gangan domin rusa su, tare da niyyar kawar da su daga doron ƙasa.
- Hana su haihuwa, ta hanyar matakan da ke rage damar ci gaban al’ummar Palasɗinawa.
Kwamitin ya ce duk waɗannan hujjoji sun fito fili ne ta hanyar nazarin kalaman shugabannin Isra’ila da kuma yadda ake tafiyar da rundunar tsaro a Gaza. Wannan, a cewar rahoton, ya isa a ɗauka a matsayin shaidar niyyar aikata kisan kare dangi.
Martanin Isra’ila
Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta yi gaggawar yin watsi da wannan rahoton, tana mai cewa “babu tushe balle makama a cikin rahoton.” Isra’ila ta jaddada cewa rundunar tsaronta na kai farmaki ne kawai kan ‘yan Hamas, ba kan fararen hula ba. Ta kuma bayyana rahoton a matsayin wani yunƙuri na rage mata ƙima a idon duniya.
Tasirin Rahoton
Rahoton na Majalisar Ɗinkin Duniya na iya ƙara matsa lamba a kan Isra’ila daga ƙasashen duniya, musamman ma daga ƙasashen da ke kiran a tsagaita wuta da kuma kare hakkin bil’adama a Gaza.
Haka kuma, rahoton na iya haifar da ƙarin matsin lamba ga manyan ƙasashe, ciki har da Amurka, wacce ita ce manyan abokan hulɗar Isra’ila.
A halin da ake ciki, ƙasashen Larabawa da dama da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun nuna goyon bayan rahoton, suna masu kira ga Kotun Ƙasa da Ƙasa (ICC) da ta ɗauki matakin shari’a kan waɗanda suka aikata laifuka.
Yayin da Isra’ila ke ci gaba da musanta zarge-zargen, rahoton UN ya sake tunzura muhawara kan makomar Palasɗinawa a Gaza da kuma matsayin Isra’ila a ƙasa da ƙasa.
Wannan na iya zama sabon juyin-juya-hali a rikicin da ya daɗe tsakanin bangarorin biyu.