KannyWood
SADIQ SANI SADIQ YA CACCAKI MASU CEWA YAN FILM SUNA KOYAR DA TARBIYA

Fitaccen jarumi na masana’antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya sake caccakar mutanen da ke zargin ’yan wasan kwaikwayo cewa suna koyar da tarbiya.
Jarumin ya bayyana cewa tarbiya abu ne da ya kamata a koya tun daga gida, saboda haka shi kudi ne yake nema a harkar fim, ba koyar da tarbiya ba.
A cikin jawabinsa, Sadiq ya kuma jaddada maganar da ya yi a watan da ya gabata, inda ya ce yana fatan ya mutu yana fim. Ya kara da cewa ko kadan bai yi nadamar furcin da ya yi ba.
A wata hira da aka yi da shi, jarumin ya sake nanata cewa, “Ni ba tarbiya nake koyarwa ba—kudi nake nema!”
Ga Bidiyon Nan