Takaitaccen Asalin Wacece Zainab Labarina a ina take, ina ne a asalin?

Daga Bakin Mai Ita shiri ne na musamman da ke tattaunawa da taurarin fina-finan Hausa da wasu fitattun mutane. A cikin shirin, mukan binciko labaransu, rayuwarsu ta yau da kullum, da irin gudunmawar da suke bayarwa ga masana’antar nishadi.
Bakuwarmu a Wannan Makon: Nana Firdausi Yahaya
A wannan makon, mun yi hira da fitacciyar jarumar Kannywood, Nana Firdausi Yahaya. An fi saninta da rawar da ta taka a matsayin matar Al’ameen a cikin shirin Labarina. Jarumar tana ci gaba da haskakawa a fina-finan Hausa masu dogon zango.
Nana Firdausi ta bayyana cewa asalinta ‘yar Jamhuriyar Nijar ce, amma tana zaune tare da iyayenta a jihar Sokoto, Najeriya. A nan ne ta yi karatunta tun daga firamare har zuwa sakandire.
A cewarta, ta samu shiga masana’antar Kannywood ne ta hanyar wani ɗan’uwanta, wanda ya kaita wajen Aminu Saira, babban darakta kuma wanda ta ke yi wa kallon ubangida a masana’antar.
Fim ɗinta na farko da ta fara fitowa shi ne Labarina, wanda ya sanya ta shahara kuma ya bude mata kofar shigowa cikin fina-finan Hausa.
Za ku iya sauraron cikakken hirar da aka yi da ita a cikin shirin Daga Bakin Mai Ita!