Blog

Tantance Wa’azi a Kano: Rikicin Kalaman Malamai da Bukatar Sabon Doka

Rikicin Kalaman Malamai da Batun Dokar Tantance Wa’azi a Kano

Faruwar al’amura masu alaƙa da addini da kuma yadda suke jawo tarzoma a Kano na ƙara jefa tambayoyi: shin akwai buƙatar samar da dokokin da za su kula da wa’azi a jihar?

A ranar Larabar da ta gabata, dubban mazauna Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana zuwa gidan gwamnati, suna ƙorafi kan zargin kalaman da suka kira “rashin ladabi” ga Annabi Muhammadu (SAW).

Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun irin waɗannan cece-kuce ba. A lokuta da dama, ana samun zarge-zargen da ke jawo muƙabala tsakanin malamai ko kuma cin gaban shari’a a kotu.

A makon da ya gabata ma, gwamnatin jihar Neja ta sanar da shirin tantance hudubar malamai da limaman coci. Ta bayyana cewa manufar hakan ita ce dakile kalaman da kan iya tunzura jama’a. Sai dai abin tambaya a nan shi ne: ko Kano ma na buƙatar irin wannan doka?

Me Ya Faru a Kano?

A ranar Laraba, wasu mazauna birnin Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana kan zargin cewa Sheikh Lawan Abubakar Triumph ya yi kalaman da ba su dace ba game da Annabi Muhammadu (SAW).

See also  Garba Muhammad: Daga Cikon Benci Zuwa Tauraro a Fim

Masu zanga-zangar sun taru a kofar gidan gwamnati, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓe su tare da yin jawabi.

A wani bidiyo da ya yaɗu a baya-bayan nan, an ga malamin yana musanta labarin cewa haihuwar Annabi Muhammadu da shayinsa wani abin al’ajabi ne. A cewarsa, ba karama ba ce, domin ana iya samun irin hakan a haihuwar sauran mutane. Ya ƙara da cewa ruwayoyin da ke nuna hakan ba su da inganci.

Martanin Gwamnan Kano

ɗalibai a aji suna murna bayan NECO 2025 yayin da Jihar Kano ta bayyana nasarar yawan masu cin jarabawa.
Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci masu zanga-zangar da su kwantar da hankali. Ya roƙe su da su rubuta takardar koke a hukumance ta hannun ofishin sakataren gwamnati.

“In Allah ya yarda, za mu ɗauki matakin da bai saba wa Shari’a ba,” in ji shi.

Gwamnan ya ƙara da cewa: “Ku rubuta takarda ta hukumance, ita ce za mu yi amfani da ita daga nan har zuwa ƙolin ƙoli.”

Masu ƙorafin sun amince za su gabatar da takardar da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Alhamis.

Ra’ayin Malamai a Kano

BBC ta tuntubi wasu malamai guda biyu a Kano. Duk da sun buƙaci a sakaya sunayensu, sun bayyana ra’ayoyi mabambanta.

Malami na farko ya ce:
“Tuni ya kamata gwamnati ta samar da doka ta wa’azi domin tantance abin da ya dace da abin da bai dace ba. Haka kuma ya kamata a fayyace akan wace mazhaba malaman Kano za su koya, tare da tantance littafan da ake amfani da su.”

See also  President Tinubu brought Ali Nuhu to his government to develop the country's economy through culture ~ Minister Bagudu

Sai dai wani malami daban ya yi adawa da hakan:
“Babu buƙatar gwamnati ta shiga harkar malamai. Idan hakan ta faru, siyasa za ta shigo. Kuma idan malami bai goyi bayan gwamnati ba, za a iya ɗaukar matakin hukunta shi. Amma gaskiya malamai suna sakin baki fiye da kima, suna rikita fahimtar jama’a.”

Abin da NSCIA Ta Bukata

A watan Fabrairu 2025, Majalisar Ƙoli ta Harkokin Shari’ar Musulunci a Najeriya (NSCIA), ƙarƙashin Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta yi kira da a samar da dokokin da za su tantance masu wa’azi a faɗin ƙasa.

Bayan taro, Sakatare Janar na Jama’atu Nasril Islam (JNI), Farfesa Khalid Aliyu, ya bayyana cewa lokaci ya yi a tsara wa’azi:

“Kar a mayar da minbarin tafsiri wurin habaici da zage-zage. Wa’azi ya kamata ya kasance bisa ilimi da gaskiya, ba kwaikwayo a gaban kyamara kawai ba.”

Shi ma wani sakatare, Malam Nafi’u Baba-Ahmed, ya ce:
“Wajibi ne gwamnati ta samar da dokoki da za su tsara wa’azi da tafsiri. Yanzu haka, wasu suna fitowa suna magana bisa jahilci suna kira kansu malamai.”

Me Kundin Tsarin Mulki Ya Ce?

Lauya mai zaman kansa a Kano, Barista Sulaiman Magashi, ya bayyana cewa tsarin mulki ya yarda mutum ya yi wa’azi, amma hakan ba ya nufin a yi shi ba tare da tsari ba.

See also  Rarara Builds Three Primary Schools In Katsina State

“Akwai buƙatar a tsara wa’azi, domin shi ma sana’a ce wadda shari’ar Musulunci da tsarin ƙasa suka amince da ita. Amma ba a ba wa kowa dama ya yi amfani da wa’azi wajen tayar da tarzoma ko cin mutunci ba,” in ji shi.

Sai dai ya ja kunne cewa, idan aka yi irin wannan doka, ya zama wajibi a saka masu ruwa da tsaki ciki, tare da guje wa siyasa ko nuna bambanci.

Lokutan Da Kalaman Malamai Suka Tunzura Kano

  • Yuli 2025: Rundunar ƴansandan Kano ta gayyaci Sheikh Lawal Triumph bayan wasu sun nemi a halatta jininsa saboda zargin kalaman rashin ladabi ga Annabi (SAW). Rikicin ya kusan jefa jihar cikin tashin hankali.
  • Yuli 2021: Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya fuskanci zarge-zargen batanci ga Annabi (SAW). Rikicin ya haifar da muƙabala da shari’a, wanda daga ƙarshe aka yanke masa hukuncin kisa.

Rikice-rikicen da suka shafi malamai a Kano na ƙara ƙarfafa muhawara kan ko ya dace gwamnati ta kafa doka ta musamman don tsara wa’azi. Wasu malamai da shugabannin addini sun nuna goyon baya, yayin da wasu ke ganin hakan zai buɗe ƙofa ga siyasa.

Abin da ya rage shi ne yadda gwamnati za ta samu daidaito tsakanin kiyaye ‘yancin addini da kuma samar da doka da zata ke tantance wa’azi da hana wa’azi zama hanyar tayar da tarzoma ko rikita jama’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks