Nico Williams Ya Tsawaita Kwantiraginsa da Athletic Bilbao Har Shekara ta 2035

Tauraron dan wasan Sifaniya, Nico Williams, ya amince da sabunta kwantiraginsa da kungiyar Athletic Bilbao har zuwa shekara ta 2035.
A cewar kungiyar, Williams ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da ta ƙara masa shekara takwas daga kwantiragin da yake da shi wanda da farko zai kare a 2027.
An Ƙara Farashin Fansarsa
Sabon kwantiragin ya tabbatar da cewa farashin fansar Nico Williams zai tashi da ƙarin kashi 50, inda yanzu ya kai aƙalla Yuro miliyan 60. Wannan zai kara wa kungiyar kima idan har wata ƙungiya ta nemi siyan dan wasan.
Nico: “Ina Nan Inda Zuciyata Ke So”
A yayin da yake bayyana farin cikinsa, Nico Williams ya ce:
“Idan lokacin ɗaukar mataki ya zo, abu mafi muhimmanci shi ne ka bi zuciyarka. Ina nan inda nake so, tare da mutanena – nan ne gidana.”
Barcelona Ta Yi Yunkurin Daukarshi
Tun kafin sanarwar sabunta kwantiragin, rahotanni sun nuna cewa Barcelona ta yi ƙoƙari na daukar dan wasan. Wasu majiyoyi sun ce har an kusa kammala ciniki kafin Athletic Bilbao ta fito da wannan sabuwar sanarwa.