Leverkusen Ta Kori Erik Ten Hag Bayan Kwana 62 Kacal

Tsohon kocin Manchester United, Erik Ten Hag, ya kasa ɗorewa a matsayin mai horas da Bayer Leverkusen har tsawon makonni goma. An sallame shi bayan kwana 62 kacal, tare da jagorantar wasanni biyu na Bundesliga kawai.
An kori Ten Hag ne bayan Leverkusen ta tashi kunnen doki 3-3 da Werder Bremen, duk da cewa ta fara cin 3-1 kuma abokin hamayyarta ya samu jan kati. Wannan ya zo ne bayan kashin farko da ƙungiyar ta sha a hannun Hoffenheim a gasar Bundesliga.
Ten Hag ya samu nasara a wasa guda kacal kafin a raba gari da shi. An ɗauke shi a watan Mayu domin maye gurbin Xabi Alonso wanda ya koma Real Madrid. Duk da fatan zai sake gina ƙungiyar da ta rasa fitattun ‘yan wasa kamar Florian Wirtz da Jonathan Tah, abubuwa sun tafi akasin haka.
Matsalolin Da Suka Jawo Rikici
- Ya sauya ranar wasan sada zumunta a Brazil, inda Leverkusen ta sha kashi 5-1 daga Flamengo U-20.
- Ya shiga sabani kan tafiyar Granit Xhaka, duk da cewa ƙungiyar ta riga ta amince ya baro.
- Ya yi tsokaci kan rashin kuzari da ƙwarewar ƴan wasansa.
- An zarge shi da rashin kwarjini da iya jawabi kafin wasanni.
Saboda waɗannan matsaloli, shugabannin ƙungiyar suka yanke shawarar raba gari da shi cikin gaggawa, abin da ya jefa Leverkusen cikin ruɗani.
Masu Iya Maye Gurgunsa
A yanzu, rahotanni na cewa ƙungiyar ta fara tattaunawa da tsohon kocin Barcelona Xavi, da kuma tsohon kocin Dortmund Marco Rose.
Ko wane ne zai karɓi ragamar, ba za a manta da gajeriyar zangon Ten Hag ba a Leverkusen cikin sauƙi.