TIN a Najeriya: Mece Ce, Yadda Ake Samunta, da Muhimmancinta
A kwanakin baya, gwamnati ta fitar da sanarwa wadda ta haifar da ruɗani a tsakanin al’ummar Najeriya. Sanarwar ta bayyana wajabcin mallakar Tax Identification Number (TIN) ga ‘yan ƙasa domin samun damar yin hulɗa da asusun banki a nan gaba. Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce, musamman daga masu ƙaramin ƙarfi da ba su fahimci ainihin manufar tsarin ba.
Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan gyaran fuska ga sha’anin kuɗi da haraji, Taiwo Oyedele, shi ne ya fara sanar da wannan batu. Amma daga baya sai ya yi karin bayani cewa wajabcin lambar TIN ba ya shafar kowa da kowa. A cewarsa, tsarin ya taƙaita ne ga mutanen da suke da wajibcin biyan haraji – ko dai ta hanyar aiki, kasuwanci, hannun jari ko wata hanyar samun kuɗi.
Mece Ce Lambar TIN?
Hukumar karɓar haraji ta Najeriya (FIRS) ta bayyana TIN a matsayin lamba ta musamman mai ɗauke da haruffa guda 13 wadda ake bai wa masu biyan haraji domin a gane su cikin sauƙi.
- Kowanne mai biyan haraji yana da lambar guda ɗaya kacal, wadda ke da nufin gane shi a ko’ina cikin ƙasar.
- Lambar TIN tana taimaka wa hukumomi wajen bin diddigin harajin da mutum ko kamfani ke biya a tsawon lokaci.
- Hakanan tana tabbatar da cewa babu wanda ya tsallake biyan abin da ya wajaba.
Wa Ya Kamata Ya Mallaki Lambar TIN?
Duk wanda ke samun kuɗaɗen shiga a Najeriya – ta hanyar:
- Aikin gwamnati ko na kamfani,
- Kasuwanci mai zaman kansa,
- Hannun jari ko wata hanyar samun kuɗi,
…ya zama wajibi ya mallaki TIN domin bin doka da tabbatar da adalci wajen karɓar haraji.
Yadda Ake Samun TIN
Hukumar FIRS ta bayyana hanyoyin da za a iya samun TIN kamar haka:
- Ta yanar gizo: Yin rijista a shafin Joint Tax Board (JTB).
- Ta ofishin FIRS ko na jihar: Mutum zai iya kai ziyara kai tsaye domin cikawa.
- Ta ejan na musamman: Ana iya amfani da wakilai da aka tantance domin taimakawa wajen yin rijista.
Abubuwan Da Ake Buƙata Domin Rijista
Domin yin rijistar TIN, mutum na buƙatar:
- Takardar haihuwa ta gaskiya,
- Lambar BVN daga banki,
- Tsohuwar TIN (ga wanda ya riga ya mallaka),
- Da sauran bayanan da suka dace da matsayin mutum ko kamfani.
Shin Ba Tare Da TIN Ba Ba Za A Iya Hulɗa Da Banki Ba?
Akwai jita-jitar cewa nan gaba idan mutum bai da TIN ba, to ba zai iya saka ko cire kuɗi daga asusunsa na banki ba. Wannan labari ya tayar da hankalin mutane, musamman talakawa.
Amma mai magana da yawun shugaban FIRS, Aderonke Atoyebi, ta yi karin bayani cewa wannan magana ba gaskiya ba ce. A cewarta:
“TIN an keɓe ta ne kawai ga mutanen da suke da wajibcin biyan haraji. Ba ta shafi waɗanda ba a cire musu haraji daga abin da suke samu ba.”
Dalilin Gwamnati Kan TIN
Gwamnati ta bayyana cewa tsarin TIN wani muhimmin ɓangare ne na gyaran fuska da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kai a watan Janairu 2026.
Manufar shi ne:
- Gano yawan masu samun kuɗaɗe a ƙasar,
- Tantance adadin kuɗaɗen da ya kamata a biya a matsayin haraji,
- Tabbatar da cewa tsarin karɓar haraji bai samu tangarda ba,
- Kuma tabbatar da adalci a tsakanin al’umma.
A taƙaice, TIN wata hanya ce da gwamnati ke amfani da ita domin tabbatar da cewa kowa ya bayar da harajin da ya dace da shi, ba tare da ɓata lokaci ko samun tasgaro a tsarin gudanar da kuɗaɗen ƙasa ba.
Wannan tsarin na TIN dai yana ɗaya daga cikin shirye-shiryen gwamnati wajen tabbatar da cewa tattalin arziƙin ƙasa ya samu ƙarfi, kuma gwamnati ta iya amfani da kuɗaɗen haraji wajen samar da ayyukan raya ƙasa da walwalar al’umma.












