Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a birnin Paris a yayin hutun aikin da yake yi a Turai.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga, ya wallafa hotunan ganawar a shafin X, inda ya bayyana cewa Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu domin cin abincin rana a fadar Elysee.
Tinubu ya bar Najeriya a makon da ya gabata domin fara hutun kwanaki 10, wanda zai shafe shi a Birtaniya da Faransa. Wannan dai ba shi ne karon farko da Tinubu zai gana da Macron ba, tun bayan hawan sa kan mulki a 2023.

Hulɗar diflomasiyya tsakanin Faransa da ƙasashen Afirka da dama ta yi tsami a ‘yan shekarun nan, musamman bayan juyin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar, maƙwabciyar Najeriya, a watan Yuli na 2023.
Ganawar Tinubu da Macron na iya zama wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar Najeriya da Faransa a bangaren tattalin arziki da diflomasiyya, duk da ƙalubalen da ke akwai a nahiyar Afirka.

















