A makon da ya gabata ne, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓen ƙasar ta 2026, wadda aka yi wa gyaran fuska. Shugaban ya sa hannu kan dokar – wadda ta ƙunshi ƙa’idojin yin zaɓukan tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukumomin yankin birnin tarayya.
A lokacin sanya hannu kan dokar, Tinubu ya ce: “Babu batun siyasa a cikin wannan gyare-gyare, abu ne na tsari, ƙoƙari ne na cike giɓi da ƙarfafa tsari da kuma samar da tsaftatacciyar hanya ga masu tsarawa da kuma masu yin zaɓuka.”
Shugaban ya sanya hannu kan dokar ne bayan hargitsin da aka samu a zaurukan majalisar tarayyar ƙasar da ma zanga-zangar da ƙungiyoyin fararen hula suka yi game da gyaran da aka yi wa dokar.
‘A Yanzu Babu Dalaget’
Ɗaya daga cikin manyan gyare-gyaren da aka yi wa dokokin zaɓen shi ne hanyoyin da jam’iyyu ke bi wajen zaɓukan fitar da gwani. A baya, jam’iyyun siyasa kan yi amfani da wasu wakilai na musamman da ake kira ‘deliget’, waɗanda ake zaɓa a matakai daban-daban, tun daga matakin akwati da mazaɓa har zuwa matakin ƙasa.
Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero da ke Kano ya ce a gyaran fuskar da aka yi wa dokar zaɓen ta 2026, an rusa wannan tsari na dalaget. A ra’ayinsa, tsarin “deliget na daga cikin abubuwan da suka gurɓata tsarin fitar da ƴantakara da ma zaɓen Najeriya baki ɗaya.”
“Saboda su deliget ɗin nan, idan suka je zaɓen fitar da gwani ciniki suke yi, sukan karɓi kuɗin kowane ɗan takara, kuma idan ba su zaɓe shi ba ba za su mayar masa da kuɗinsa ba,” in ji shi.
A yanzu, sabuwar dokar ta tanadi hanyoyi guda biyu na gudanar da zaɓukan fitar da gwani na ƴantakara, wato: masalaha da ƴar tinƙe (ƙato-bayan-ƙato).
Me Ake Nufi da Masalaha?
Masalaha shi ne masu sha’awar tsayawa takarar gujera ɗaya a jam’iyyar ɗaya su zauna tsakaninsu su yi sasanci domin janye wa mutum guda. A wannan zama, ƴantakarar da shugabannin jam’iyyu za su zauna tare da ƙulla alƙawura domin cimma yarjejeniya.
Sabuwar dokar ta yi tanadin cewa idan wannan hanya ba ta kai ga nasara ba, to sai a je hanya ta biyu — wato ƴar tinƙe.
Me Ake Nufi da Ƴar Tinƙe?
Farfesa Fagge ya bayyana cewa a ƴar tinƙe, ƴan jam’iyya masu rajista za su fita domin zaɓen mutumin da suke so ya tsaya wa jam’iyyar takara. Akan gudanar da wannan zaɓe a matakai daban-daban, kama daga mazaɓu zuwa ƙaramar hukuma, jiha, da kuma matakin tarayya.
Hanyoyin biyu na ƴar tinƙe su ne: bi layi a bayan ɗantakarar da ake so a ƙirga yawansu, ko kuma zaɓe a asirce ta amfani da akwati.
A Ina Za a Yi Zaɓukan?
A baya, akan gudanar da zaɓukan fitar da gwanaye a manyan tarukan jam’iyyun. A yanzu ma haka za a yi, amma a matakai daban-daban — daga matakin mazaɓa zuwa ƙaramar hukuma da jiha.
A matakin zaɓen gwamna ko shugaban ƙasa, za a gudanar da zaɓukan a wurare daban-daban a rana guda. “Idan za a yi na gwamnoni saboda yawan ƴan jam’iyyar za a gudanar da zaɓukan ne a kowace ƙaramar hukumar, haka ma na shugaban ƙasa za a yi a kowace jiha,” in ji Farfesa Fagge.
‘Shi Ma Tsarin Na Da Nasa Matsaloli’
Manufar yi wa dokar gyara dai shi ne magance matsalolin da ake yawan samu a zaɓukan fitar da gwanaye — lamarin da a wasu lokutan ke ƙarewa a kotuna, ko ma ya janyo asarar kujerun da jam’iyyar ta riga ta ci a babban zaɓe. Alal misali, a shekarar 2019, jam’iyyar APC ta rasa kujerun gwamna da na majalisar dattawa da ta wakilai a jihar Zamfara bayan matsaloli masu alaƙa da zaɓukan fitar da gwani.
Duk da haka, Farfesa Fagge ya gargaɗi cewa sabon tsarin ma yana ƙunshe da nasa matsalolin. “A wasu lokutan ƴan takara kan karɓi katunan jam’iyyar daga hannun ƴan jam’iyyar ta hanyar ba su kuɗi, sai kuma ya kira wasu da ma ba ƴan jam’iyyar ba ya ba su kuɗi da waɗannan katuna domin su zaɓe shi.”
Har ila yau, ya ce ƴan takara sukan tayar da fitina a lokacin ƙirge-ƙirge — musamman idan suka hango cewa abokin hamayyarsu na kan gaba — har ta kai ga dakatar da aikin ƙirge-ƙirge da zargin magudi.





