Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarni ga wani kwamitin gwamnatin tarayya da ya ɗauki gaggawar matakai don rage farashin kayan abinci a faɗin ƙasar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ministan Jiha na harkokin noma da tsaron abinci, Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a Abuja.
Ya ce, umarnin shugaban ƙasa ya fi karkata ne wajen tabbatar da kariya da sauƙin jigilar kayan gona a manyan hanyoyin ƙasar.
“Shugaban ƙasa ya bayar da cikakken umarni tare da kafa wani kwamiti da ke kula da yadda za a samar da kariya da kuma sauƙaƙa jigilar kayan abinci,” in ji Abdullahi.
Ministan ya ƙara da cewa wannan matakin yana cikin hangen nesan Tinubu na kai Najeriya ga cin gashin kai a fannin abinci.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati na shirin ƙaddamar da wani tsari mai suna “Farmer Soil Health Scheme”, wanda zai ƙara yawan amfanin gona da kuma sabunta tsarin haɗin kan manoma, domin su haɗa albarkatu tare da ƙarfafa manoman karkara.
“Shugaban ƙasa ya nuna matuƙar sha’awa a tsarin haɗin kan manoma a matsayin hanya ta tara albarkatu, samar da ayyukan tattalin arziki, da inganta rayuwar manoma,” in ji Abdullahi.


























