Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa zai saka Najeriya cikin jerin ƙasashe “da ake da damuwa a kansu” saboda zargin yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla a ƙasar.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce “shi ne mataki mafi ƙanƙanta da ya dauka” domin kare addinin Kirista.
“Kiristanci na fuskantar babbar barazana a Nageria,” in ji shi. “Ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke aikata hakan. Saboda haka na ayyana Najeriya a matsayin ƙasa da ake da damuwa a kanta.”
Trump ya kuma bayyana cewa ya bai wa ‘yan majalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole umarnin su gudanar da bincike a kan lamarin sannan su gabatar masa da rahoton sakamakon binciken nasu.
A farkon watan nan, wani sanata a Amurka ya zargi gwamnatin Nageria da yin shiru kan kisan Kiristoci, lamarin da gwamnatin Najeriya ta musanta, duk da cewa batun ya haifar da muhawara mai zafi a ƙasar.
Najeriya ce ƙasa mafi yawan jama’a a Afirka, kuma mafi fitar da ɗanyen mai, abin da ke sa irin wannan mataki na iya yin tasiri a fannin siyasa da tattalin arziƙi.
Me Wannan Ke Nufi?
Bisa bayanin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, ana ayyana ƙasa a matsayin “ƙasar da ake da damuwa a kanta” idan aka tabbatar tana tauye ‘yancin addini bisa Dokar ‘Yancin Addini ta Duniya (IRFA) da aka kafa a 1998.
“Amurka tana da nauyin bayyana halin da ake ciki kan ‘yancin addini a duniya, domin a samu hanyoyin magance matsalolin take hakkin addini,” in ji ma’aikatar a shafinta na intanet.
A cewar dokar, idan ƙasa ta shiga wannan jerin, za a iya ƙaƙaba mata takunkumi a fannoni kamar tattalin arziƙi da makamai, a matsayin hukunci.
Abin Da Masana Ke Faɗi
A wata tattaunawa da BBC, masanin tsaro a Afirka Bulama Bukarti ya ce akwai manyan illoli uku da Najeriya za ta iya fuskanta idan aka ayyana ta a matsayin ƙasa da ake da damuwa a kanta.
1️⃣ Daina sayar wa Najeriya makamai
Bukarti ya bayyana cewa Amurka da ƙawayenta za su iya dakatar da sayar da makamai, jiragen yaƙi da sauran kayan tsaro da Najeriya ke amfani da su wajen yaƙar ‘yan ta’adda.
2️⃣ Takunkumin tattalin arziƙi
Ya ce hakan zai shafi fannin tattalin arziƙi, inda ƙasashen waje za su iya daina sayen ɗanyen man Najeriya, da kuma daina sayar mata da kayan masarufi.
Najeriya, wacce ke dogaro sosai da kuɗaɗen man fetur da shigo da kaya daga waje, na iya fuskantar tsadar abinci da durƙushewar darajar kuɗi.
3️⃣ Ƙara tsanantuwar rikicin addini
Bukarti ya ƙara da cewa idan Amurka ta amince da ikirarin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya, hakan zai iya tayar da ƙarin husuma tsakanin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban a cikin ƙasar.
A shekarar 2021, Amurka ta cire sunan Najeriya daga jerin ƙasashen da ake da damuwa a kansu, amma sabbin kiraye-kiraye daga wasu ƙungiyoyi na iya sa Trump ya sake mayar da sunan ƙasar cikin jerin.
Matsayin Gwamnatin Najeriya
Tun a watan Satumban 2025, gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa ana kisan ƙare-dangi kan mabiya addinin Kirista.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce “ba gaskiya ba ne” rahotannin da wasu kafafen labarai da shafukan sada zumunta ke yadawa, yana mai cewa matsalar tsaro ta ƙasar ba ta takaitu ga addini ko ƙabila ɗaya ba.
“Gwamnati ta yi Allah-wadai da waɗannan zarge-zargen. Ayyukan ‘yan ta’adda suna shafar dukkan ɓangarori na ƙasar — Musulmi da Kirista, Arewa da Kudu,” in ji shi.
Matsalar Tsaro a Najeriya
Najeriya ta kwashe fiye da shekaru 15 tana fama da matsalolin tsaro, musamman rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabas wanda ya hallaka dubban mutane da raba miliyoyi da muhallansu.
Ƙungiyar Boko Haram ta fara ne da da’awar adawa da karatun boko, amma daga bisani ta koma kai hare-hare kan jami’an tsaro, fararen hula, da wuraren ibada — masallatai da majami’u.
Hare-haren ta sun haɗa da sace ɗalibai da garkuwa da su, kamar yadda aka gani a Cibok a 2024.
Baya ga Boko Haram, akwai rikicin manoma da makiyaya a tsakiyar ƙasar wanda ke jawo asarar rayuka da dukiya, musamman a jihohin Filato da Benue.
Ƴan fashin daji da masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma na ci gaba da barazana, yayin da rikicin ‘yan awaren Biafra ke ƙara ƙone yankin Kudu maso Gabas.
Duk da haka, gwamnatin Najeriya na cewa tana ƙoƙarin kawo karshen waɗannan matsaloli ta hanyar haɗin gwiwa da ƙasashen waje da kuma ƙarfafa jami’an tsaro.

















