Nishadi

“Tunda samari sun ƙi yiwa ƴan mata Ramadan Basket, mai zai hana mata kuyi ku kaimasu ku gani ko zasu karɓa, babu kunya ~ cewar Jaruma Ayshatul Humaira”

Jaruma Ayshatul Humaira Ta Kira Ƴan Mata Da Su Ba Samari Ramadan Basket

Fitacciyar mai amfani da kafafen sada zumunta, Jaruma Ayshatul Humaira, ta bayyana ra’ayinta game da al’adar Ramadan Basket. Ta ce tunda samari sun ƙi yi wa ƴan mata kyautar Ramadan Basket, me zai hana ƴan mata su yi wa samarin kuma su kai musu?

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Instagram, ta ƙalubalanci samari da cewa idan har ƴan mata sun kawo musu kyautar Ramadan Basket, za su karɓa kuwa? Ko kuwa za su ji kunya su amsa daga hannun mata?

Ta ci gaba da cewa tunda samari sun ƙi yin hakan ga ƴan matansu, lokaci ya yi da ƴan mata za su gwada musu su gani ko za su nuna halin ko-in-kula ko kuwa za su karɓa da farin ciki. Wannan batu ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke goyon baya yayin da wasu ke sukar wannan tunani.

Meye Ra’ayinku?

Shin kun yarda da cewa lokaci ya yi da ƴan mata za su mayar da martani ga samari ta hanyar ba su Ramadan Basket? Kuma idan hakan ta faru, samari za su karɓa kuwa? Ku bayyana ra’ayoyinku a sashin sharhi!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button