YADDA ALI NUHU YA SHIGO DA RAHAMA SADAU MASANA’ANTAR KANNYWOOD

ALI NUHU YA SHIGO DA RAHAMA SADAU KANNYWOOD
Fitacciyar jarumar finafinan Hausa, Rahama Sadau, ta bayyana cewa Ali Nuhu ne ya kawo ta masana’antar Kannywood. Rahama ta yi wannan bayanin ne a wata hira da ta yi da Aminu Sherif Momo a cikin shirin Kundin Kannywood.
Rahama ta ce Ali Nuhu ya gan ta tana rawa a wani gidan rawa a Kaduna, inda ya nuna sha’awarsa ga baiwar rawar da take da ita, sannan ya dauko ta ya shigar da ita harkar fim. A cewarta:
“Ban san shi ba. Wata rana ne ya same ni ina rawa, sai ya ce ai wanda zai iya rawa zai iya fim.”
YADDA RAHAMA SADAU TA FARA RAWA
Rahama ta bayyana cewa ta fara koyon rawa ne tun tana makarantar sakandare, inda ta shiga ƙungiyoyin rawa a Kaduna. Bayan haka, ta shiga wani rukuni na masu rawa inda suke yin rawar Indiya da kuma rawar titin. Ta ce:
“A sakandare na fara koyon rawa. Na shiga irin ƙungiyoyin nan na makaranta. Da na gama sakandare sai na shiga wata ƙungiyar ‘yan rawa a Kaduna.”
TSAYAYYAR ALAKA TSAKANIN ALI NUHU DA RAHAMA SADAU
Rahama Sadau ta kara da cewa akwai dangantaka mai karfi tsakaninta da Ali Nuhu har yanzu. Ali Nuhu dai shi ne wanda ya karɓe ta kuma ya ba ta damar fara aikin fim, wanda daga nan ne ta samu shahara sosai a cikin masana’antar finafinai na Hausa da ma Kudancin Najeriya.