Zanga-Zangar Adawa Ta Ƙaru a Tanzaniya Bayan Rahotannin Tashin Hankali

Ana sa ran zanga-zangar adawa da gwamnati za ta ci gaba a ƙasar Tanzaniya, bayan rahotannin tashin hankali da suka barke a jiya a sassa daban-daban na ƙasar, inda aka samu rikici tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro.
Zanga-zangar ta samo asali ne daga fushin jama’a kan zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a makon nan, wanda ake zargin an hana yawancin fitattun ‘yan adawa shiga. Wannan ya janyo ƙorafe-ƙorafe daga kungiyoyi masu sa ido da jama’a.
A cikin jawabin da Shugaban Rundunar Sojin ƙasar ya gabatar a daren jiya, ya roki al’umma da su kwantar da hankali tare da guje wa tashin hankali, yana mai cewa rundunar soji tana sa ido kan duk wani yunkuri na tada zaune-tsaye.
Rahotanni daga kafafen watsa labarai sun tabbatar da cewa intanet ta ci gaba da kasancewa a katse, abin da ke hana jama’a da manema labarai samun ingantattun bayanai kan halin da ake ciki a kasar.
Ana sa ran masu zanga-zanga za su sake taruwa yau, inda suke shirin yin tattaki zuwa gidan gwamnati a birnin Dar es Salaam, yayin da ake jiran hukumar zaɓe ta fitar da sakamakon ƙarshe a ƙarshen wannan mako.
Hukumomi sun kuma ƙara tsaurara matakan tsaro a manyan birane kamar Dar es Salaam, Dodoma da Arusha, domin kauce wa rikice-rikice da ɓarna.
Har yanzu dai ba a san inda Shugabar ƙasa Samia Suluhu Hassan take ba, yayin da ake ci gaba da yaɗa jita-jita kan halin da take ciki, lamarin da ke ƙara haifar da damuwa a tsakanin jama’a.
Masu sa ido na ƙasa da ƙasa sun bayyana cewa zaɓen bai kasance na gaskiya da adalci ba, duk da cewa ana sa ran Samia Suluhu Hassan ce za ta lashe zaɓen a hukumance.