‘Ƴan Najeriya ne za su zaɓi wanda zai yi takara a ADC’

Sabuwar Haɗakar ‘Yan Siyasa ta ADC Ta Bude Kofa Ga Masu Son Tsayawa Takara a 2027
Sabuwar haɗakar ‘yan siyasa a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ce ‘yan Najeriya ne za su yanke hukunci kan wanda ya dace ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaben 2027.
Ƴan Najeriya Za Su Zabi Shugaban da Suka Yarda da Shi
Ibrahim Hussain Abdulkarim, ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan wannan sabuwar tafiya, kuma makusanci ga tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi, ya bayyana cewa za a bai wa al’umma cikakken ‘yanci wajen zaɓar wanda suka ga ya cancanta.
“Za mu bai wa ‘yan Najeriya damar zaɓar wanda suke so – wanda ke da mafita ga matsalar tsaro, talauci, da ci gaban talakawa,” in ji Abdulkarim.
Kofa A Bude Ga Masu Sha’awar Takara
Abdulkarim ya ƙara da cewa sabuwar haɗakar jam’iyyar ADC za ta buɗe ƙofa ga duk wanda ke da muradin tsayawa takarar shugaban ƙasa, inda za su bayyana manufofinsu kai tsaye ga talakawa.
Tsari da Raba Muƙamai Cikin Masalaha
Ya bayyana cewa za a raba manyan muƙamai na cikin jam’iyyar da adalci da masalaha, domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki kafin zaɓen 2027.