Ƴanta’adda sun kashe mutum 127 a hare-hare biyar a Nijar – HRW

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta duniya, Human Rights Watch (HRW), ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe sama da mutum 127 a hare-hare biyar da suka auku a yammacin Tillabéri, Nijar. Cikin waɗanda aka kashe akwai mazauna kauyuka da kuma musulmi da suka kasance cikin ibada.
An zargi ƙungiyar IS-Sahel da kai waɗannan hare-haren, inda aka ƙone gidaje, aka sace dukiyoyi, tare da barin jama’a cikin tsananin tashin hankali.
HRW ta ce, hare-haren sun saɓa wa dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, tare da zama abin da ake iya ɗauka a matsayin laifukan yaƙi.
Kungiyar ta kuma zargi hukumomin Nijar da gaza kare fararen hula yadda ya kamata. Rahoton ya nuna cewa sojoji ba su mayar da martani ga gargaɗin da aka yi musu ba, duk da cewa mazauna kauyuka sun nemi kariya.
Shaidu daga yankunan da aka kai hare-haren sun tabbatar cewa mayaƙan IS-Sahel ne suka kai farmakin, bisa ga kayan da suka sa da kuma barazanar da suka yi kafin kai harin.
Har yanzu, hukumomin Nijar ba su fitar da wata sanarwa kan rahoton Human Rights Watch ba.