Siyasa

APC Ta Karyata Jita-jitar Cewa Za a Sauya Mataimakin Shugaba Tinubu a 2027

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba gaskiya bane cewa Shugaba Bola Tinubu zai sauya mataimakinsa Kashim Shettima, a zaben da za’ayi 2027.

Jam’iyyar ta yi wannan bayani ta bakin mataimakin shugabanta na ƙasa daga Kudu-maso-Gabas, Dakta Ijeoma Arodiogbu. A cewarsa, wannan magana karya ce da za ta iya rikita masu goyon bayan jam’iyyar.

Arodiogbu ya ce Kashim Shettima yana da matuƙar muhimmanci a tafiyar gwamnatin Tinubu. Ya bayyana cewa waɗanda ke yaɗa wannan jita-jita ‘yan adawa ne kawai da ke son janyo rabuwar kai cikin APC.

Wannan jita-jitar ta fito ne bayan da shugabannin APC suka nuna cikakken goyon bayansu ga Tinubu. Gwamnoni 22, shugabannin majalisa, da manyan jiga-jigan jam’iyyar sun ce Tinubu shi kaɗai ne ɗan takararsu a 2027.

A Taƙaice:

  • APC ta ce ba za a sauya Shettima ba.
  • Ta kira jita-jitar ƙarya ce da ke nufin rikita jama’a.
  • Jam’iyyar na da cikakken goyon baya ga Tinubu a zaben 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button