Dakatar Da Ni Ba Zai Hana Ni Aiki A Matsayin Sanata Ba” – Natasha Akpot -Uduaghan

Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana cewa dakatar da ita daga Majalisar Dattawa rashin adalci ne kuma ba zai hana ta ci gaba da aiki ba.
Dalilin Dakatarwar
A ranar 20 ga Fabrairu, yayin zaman majalisar, an samu zazzafar muhawara tsakanin Natasha da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan batun wajen zama. Wannan sai ya haifar da ce-ce-ku-ce, har ta kai ga Natasha ta yi zargin cewa Akpabio na neman yin lalata da ita.
Biyo bayan wannan rikici, an kafa kwamitin ladabtarwa da da’a domin binciken lamarin. A karshe, kwamitin ya yanke hukuncin dakatar da Natasha na tsawon watanni shida, tare da watsi da koken da ta gabatar.
Martanin Natasha
Bayan fitar da wannan hukunci, Natasha ta bayyana cewa:
“Dakatar da ni daga majalisar dattawa ba bisa ka’ida ba ne. Wannan hukunci yana nuna tsoratarwa da muzgunawa, kuma ya karya ka’idojin adalci da gaskiya.”
Ta kara da cewa:
“Duk da wannan dakatarwa, ba za ta hana ni ci gaba da aiki a matsayina na sanata ba. Zan ci gaba da wakiltar al’ummata da kare muradun su har zuwa shekarar 2027, kamar yadda aka zabe ni.”
Lamarin dakatarwar Natasha Akpoti-Uduaghan ya haifar da muhawara mai zafi a fagen siyasa. Yanzu dai lokaci ne zai nuna irin tasirin da wannan hukunci zai haifar a harkokin majalisar dattawa da kuma siyasar Najeriya baki daya.