Nishadi

Ƙarshen Tika-Tika: Abdul M. Shareef da Maryam Malika Za Suyi Aure

Jaruman Kannywood, Abdul’azeez Muhammad Shareef (wanda aka fi sani da Abdul M. Shareef) da Maryam Muhammad Ƙaura (wadda aka fi sani da Maryam Malika) za suyi aure bayan doguwar soyayya da suka sha tare.

Za a ɗaura auren nasu ne a ranar Juma’a, 27 ga Yuni, 2025, a Masallacin Alhaji Sani Zangon Daura da ke Unguwar Kaji, hanyar Kaduna zuwa Zariya, da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

Tarihin Soyayyar Su

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Maryam Malika ta taɓa auren ƙanen marigayi mawaƙi El-Mu’az Birniwa a cikin watan Yuni, 2012. Sun haifi ‘ya’ya tare kafin suka rabu.

Bayan rabuwar ta da mijin ta na farko, soyayya ta musamman ta kunno kai tsakaninta da Abdul M. Shareef, wanda shi ɗan uwan mawaƙi ne, Umar M. Shareef.

Soyayyar tasu ta yi ƙarfi matuƙa, har wasu ke cewa Malika ba ta amsa yin fim sai idan Abdul ya bada izini.

A Halin Yanzu

A yanzu haka, Malika za ta shiga gidan Abdul a matsayin matar sa ta biyu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button