Adam A Zango Yayi Aure Ya Angonce Da Jaruma Maimuna (Salamatu) Na Shirin Garwashi

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A Zango Yayi Aure, ya aura jaruma Maimuna Musa, wacce aka fi sani da Salamatu a cikin shirin Garwashi.
Wannan bikin aure ya zo ne mako guda bayan auren da aka yi wa jaruma Rahama Sadau a Kaduna, ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, 2025.
Rahotanni sun nuna cewa furodusan shirin Garwashi, wacce kuma take mai ba wa gwamnan Kano shawara, Fauziyya D. Sulaiman, ce ta tabbatar da wannan aure a shafinta na Facebook.
Ta bayyana farin cikinta tare da addu’ar samun zaman lafiya ga ma’auratan, duk da cewa ba ta bayyana lokacin, wurin da ranar daurin auren ba.
Wata sanarwa daga DW Hausa ta tabbatar da lamarin, inda ta bayyana cewa Salamatu ta Garwashi ta amarce da fitaccen jarumin Kannywood, Adam A Zango Yayi Aure.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da jarumin ya yi aure ba, domin a baya ya yi aure sau da dama a ciki da wajen Kannywood, amma dukkan su sun kai ga rabuwa.
Tuni dai abokan sana’a da masoya na Kannywood suka fara tura sakon taya murna.
Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya taya Zango da amaryarsa murna a Instagram, inda ya yi addu’ar Allah Ya basu zaman lafiya da zuri’a nagari.
Haka zalika, Ali Nuhu, wanda aka fi sani da Sarki Ali, ya bi sahu wajen taya abokinsa murna a shafinsa na Facebook.
A bangaren masoya kuwa, da dama sun cika kafafen sada zumunta da sakonnin fatan alheri.
Wani mai suna Ibrahim Bala ya rubuta: “Masha Allah, ina taya ka murna jarumi na, Ubangiji Allah ya ba ku zaman lafiya.”
Haka nan wani mai suna Bashir Mohammed ya kara da cewa: “Allah Ya ba su zaman lafiya tare da zuri’a dayyiba, amin.”