Ƙungiyar ASUU Reshen Benin ta ƙi amincewa da sabon ƙarin albashi da Gwamnatin Tarayya ta gabatar, tana bayyana shi a matsayin “ƙwaya a teku”, musamman ganin cewa malaman jami’a ba su samu wani babban binciken albashi ba tsawon shekaru 15.
Shugaban Yankin, Farfesa Monday Igbafen, ya bayyana cewa sabon tayin da gwamnati ta yi yana kawo cikas ga burin dakatar da yawan ficewar ƙwararrun malamai zuwa ƙasashen waje (brain drain) da ke cigaba da ruguza tsarin ilimin jami’o’i a ƙasar.
Ya zargi Gwamnatin Tarayya da nuna rashin niyyar warware matsalolin da ke gaban ta gaba ɗaya, yana mai kira da ta gaggauta kammala tattaunawar yarjejeniyar 2009 FGN/ASUU tare da warware sauran batutuwan da suka dade a jingine.
Ƙungiyar ta ASUU ta fara yajin aiki na makonni biyu a baya domin matsa lamba kan gwamnati ta cika alkawuran da ta daɗe tana jinkirta.
“Mun ƙi amincewa da sabon ƙarin albashin da gwamnati ta bayar, domin ba wani abu bane face ƙananan sauyi da ba zai iya magance matsalar ficewar ƙwararru da ke kassara ilimin jami’a a ƙasar nan ba.
“Muna cewa mun gaji da yadda tattaunawar gwamnati da ASUU ke ta dawowa da komawa ba tare da sakamako ba. Wannan halin ya kamata ya ƙare.”
Farfesa Igbafen ya jaddada cewa albashin malaman jami’a ya tsaya cik tun shekarar 2009, lokacin da farashin dala yake N120.
Ya ce: “Abin takaici ne cewa abin da farfesa ke samu a yau bai kai dala $400 a wata ba, lamarin da ke nuna ƙasƙantar da ƙwarewar masana a Najeriya.
“Ci gaba da zama a kan tsarin albashi guda tsawon fiye da shekaru 15 ba tare da ingantacciyar duba ba, ba wai mugunta ba ce kawai, har ma tana haifar da tashin hankali, rashin jituwa a masana’antu da kuma ƙara yawan barin ƙasar.”
Ya kuma zargi wasu jami’an gwamnati, ciki har da ministan ilimi, da gurɓata tsarin tattaunawar ta hanyar ɓoye bayanai da nuna abubuwa ba bisa yadda suka dace ba, kamar batun biyan bashin haɓakar matsayi tun daga 2017 da kuma sakin kuɗaɗen third-party deductions da suka dade ba a biya malamai ba.
Ya ce, “Sun rinƙa gabatar da waɗannan matsalolin a matsayin manyan batutuwa, alhali a zahiri ƙananan abubuwa ne kawai da za su iya ƙara kwarin guiwa wajen tattaunawa.”
Igbafen ya bayyana cewa wannan rashin gaskiyar da ake yi wa jama’a game da tattaunawar ce ke janyo samun rikice-rikice ba tare da mafita ba.
Ya yi kira ga gwamnati ta warware matsalolin cikin watanni guda da suka rage, domin kaucewa durƙushewar tsarin.
“Gwamnatinmu ya kamata ta gane cewa babu wani abin da ya yi yawa wajen saka hannun jari cikin ilimin ’yan ƙasa, domin shi ne tushen cigaban kowane al’umma.
“Roki game da ƙarancin kuɗi ko durƙushewar tattalin arzikin duniya ba su da tushe, ganin yadda kudaden shiga na ƙasar suka karu sosai,” in ji shi.
Shugaban yankin ya kuma nuna cewa kuɗaɗen shiga na Najeriya sun ƙaru matuka a cikin ’yan shekarun nan.
Ya ce, “Adadin kudaden shiga na 2024 ya kai N5.81 tiriliyan, ƙaruwa da fiye da kashi 62%.
“Haka kuma muna da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya ta karɓi N4.65 tiriliyan a shekarar 2024, karuwa da sama da kashi 70%,” in ji Farfesa Igbafen.

















