Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, hukuncin daurin rai da rai bayan ta same shi da laifukan da ake tuhumarsa da su.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta tabbatar da samunsa da laifuka bakwai da suka shafi ta’addanci da tunzura mutane su tayar da tarzoma.
Abin Da Alƙalin Ya Ce
Alƙalin kotun, Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa, laifukan da Kanu ya aikata a zahiri sun cancanci hukuncin kisa. Sai dai ya ce:
- Kasashen duniya da dama suna nuna ƙin jinin hukuncin kisa,
- Saboda haka ya sauya hukuncin zuwa daurin rai da rai maimakon kisa.
Umarnin Da Kotun Ta Ɗara Bayarwa
Bayan yanke hukunci, alƙalin ya kuma bayar da wasu ƙarin umarni game da yadda za a ci gaba da tsare Kanu:
- A canja masa gidan yari daga na Kuje da ke Abuja zuwa wani wuri dabam, saboda a cewarsa yana da hatsari a ci gaba da ajiye shi a can.
- An haramta masa amfani da waya ko wata na’urar sadarwa.
- Idan ma za a ba shi damar wani irin sadarwa, alƙalin ya ce dole ne a sanya masa ido sosai a kowane lokaci.
Laifukan Da Ake Tuhumar Kanu Da Su
Tuhume-tuhumen da ake yi wa Nnamdi Kanu sun haɗa da:
- Laifin ta’addanci,
- Tunzura jama’a su kai hari su kashe ‘yan sanda da sojoji,
- Kasancewa mamba a haramtacciyar ƙungiyar IPOB wacce gwamnatin Najeriya ta haramta,
- Da kuma yaɗa farfagandar ta’addanci ta hanyar maganganu da saƙonnin da yake yaɗawa.
Wannan hukunci ya sake jawo cece-kuce a tsakanin al’umma, musamman masu goyon bayan Kanu da waɗanda ke adawa da ayyukan ƙungiyar IPOB.

















