KannyWood

‘Yan Sanda sun kama ‘yan fashi hudu a Bauchi bayan hari a Madina da Fadaman Mada

Rundunar ‘Yan Sanda ta Bauchi ta Kama ‘Yan Fashi Hudu

Rundunar ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi sun kama wasu mutum hudu da ake zargi da fashi da makami, daga cikin wata kungiya mai kusan mutane 20 da ta kai hari a unguwannin Madina da Fadaman Mada, ranar 16 ga Agusta, 2025.

Rahotanni sun nuna cewa miyagun mutanen, dauke da bindigogi, adduna, wukake da sanduna, sun afka wa al’ummomin da sassafe, inda suka kwace wa akalla mutum 10 kayayyaki masu daraja. Abubuwan da suka sace sun hada da wayoyin hannu 14, talabijin guda biyu, kaya na maza guda biyu, da kuma kudi har naira 100,000.

Mai magana da yawun rundunar, Ahmed Wakil, ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar. Ya bayyana cewa da misalin karfe 03:20 na dare, rundunar ta samu kiran gaggawa daga wani da ba a bayyana sunansa ba, yana sanar da cewa kusan ‘yan fashi 20 sun kai farmaki tsakanin karfe 02:00 zuwa 03:00 na dare. Sun shiga gidaje da dama inda suka kwace kayayyaki masu daraja tare da tsoratar da mazauna yankin.

See also  Dalilin Da Ya Sa Muka Daina Haska Shirin "Labarina" a Arewa24

Da zarar jami’an sashen C Division, karkashin jagorancin DPO, suka isa wurin tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai, ‘yan fashin suka tsere suka bar wasu daga cikin kayan da suka sace.

Wakil ya kara da cewa daga baya, da misalin karfe 05:03 na asuba, jami’an leken asiri suka kama daya daga cikin wadanda ake zargi, Ahmed Hassan, mai shekaru 20, dan unguwar Tirwun a Bauchi. An kama shi a Warinje Hills da wayar hannu kirar Gionee da aka sace a hannunsa.

Bayanin da ya bayar ya taimaka wajen cafke sauran mutum uku:

  • Ismail Isah, mai shekara 18 (wanda aka fi sani da Masha),
  • Uzaifa Abubakar, mai shekara 19 (wanda aka fi sani da Damo),
  • Abdulhamid Idris, mai shekara 20.
See also  JARUMA MARYAM YAHAYA TA SIYA SABON MOTA

Kayan shaidar da aka kwato sun hada da bindigar kera gida kirar revolver, harsashi daya na 7.62mm, bindigar gida gajera (Dane gun), wuka, adduna guda biyu, da fitila.

Wakil ya bayyana cewa a yayin bincike, wadanda aka kama sun amsa cewa suna da hannu a wasu ayyukan fashi da makami a cikin Birnin Bauchi. Yanzu haka ana ci gaba da bin diddigin sauran abokan harkarsu domin cafke su. “Bayan kammala bincike, za a gurfanar da su a gaban kotu,” in ji shi.

Wannan cigaba na zuwa ne yayin da rundunar ke kara tsaurara matakan yaki da laifuka a Bauchi. A baya-bayan nan, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Sani Omolori-Aliyu, ya bayyana cewa an kama mutane 748 da ake zargi da hannu a cikin laifuka 394 cikin watanni takwas da suka gabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks