HUKUMAR TACE FINA-FINAI TA KANO TA DAKATAR DA WASU JARUMAI DA MAWAKI

Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, karkashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta dakatar da wasu jarumai mata uku da kuma mawaki Usman Soja Boy. Wannan hukunci ya biyo bayan zarge-zargen rashin da’a, batsa, da kuma sanya tsiraici a bidiyoyin da suka wallafa a kafafen sada zumunta.
Sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya bayyana ta ce an haramta tace duk fina-finai ko waÆ™oÆ™in da waÉ—annan jaruman suka fito a ciki.
- SAMHA M. INUWA
Hukumar ta dakatar da jaruma Samha M. Inuwa na tsawon shekara guda bisa dalilan da suka haÉ—a da:
Sanya tufafin da suka saba tarbiyya.
Wallafa bidiyoyin da ke nuna tsiraici.
Rahotanni sun nuna cewa jarumar ta sha gargaÉ—i daga hukumar kan irin halayenta, amma ta Æ™i gyara. Bidiyon da ya jawo matsala ya nuna tana sanye da tufafi masu bayyana surar jikinta, wanda hakan ya haifar da cece-kuce a tsakanin jama’a.
- USMAN SOJA BOY
Hukumar ta dakatar da mawakin Kannywood, Usman Soja Boy, bisa dalilin wallafa bidiyoyi masu É—auke da batsa. Sanarwa ta nuna cewa:
An kwace lasisinsa na aiki a Kannywood.
An haramta tace fina-finai ko waƙoƙin da ya fito a ciki.
Duk da haka, mawakin ya yi ikirarin cewa dakatarwar ba ta dame shi ba, yana mai cewa shi ne ya fi taimakawa masana’antar, ba akasin haka ba.
- WASU JARUMAI MATA BIYU
Baya ga Samha M. Inuwa da Usman Soja Boy, wasu jarumai mata biyu da suka fito a cikin bidiyoyin mawakin sun haÉ—u da hukuncin dakatarwa. Duk da haka, babu cikakken bayani a kan sunayensu ko irin laifukan da suka aikata, amma hukumar ta tabbatar da cewa sun karya dokokin tace fina-finai.