Siyasa

ADC Ta Koka Ana Hana Ta Taruka a Wasu Jihohin Najeriya

Jam’iyyar hamayya ta ADC ta koka ta yi zargin cewa ana hana mambobinta gudanar da taruka a wasu jihohi, lamarin da shugabanninta suka ce ya saba wa kundin tsarin mulkin ƙasa.

Shugabannin jam’iyyar na ƙasa sun bayyana haka a wani taro da suka yi a Kaduna ranar Alhamis. Sun bukaci a gudanar da bincike tare da hukunta wadanda suka kai hari ga mambobinsu a jihohin Kaduna, Kebbi da Katsina, inda aka jikkata wasu.

Ziyarar Jajantawa

Tawagar shugabannin jam’iyyar ta ce ta ziyarci Kaduna domin jajanta wa reshen jihar, bayan wasu gungun makamai sun kai hari a lokacin taron jam’iyyar makon da ya gabata. Duk da cikas da suka fuskanta wajen halartar taron, sun ce ba zai karya musu guiwa ba.

See also  APC Ta Karyata Jita-jitar Cewa Za a Sauya Mataimakin Shugaba Tinubu a 2027

Tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce an hana su amfani da sakatariyar jam’iyyar a Kaduna bisa wani umarnin kotu da kwamishinan ‘yan sanda ya ce ya samu. Saboda haka suka taru a gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, domin gabatar da alhinin su.

Tambuwal ya kara da cewa abin takaici ne yadda aka kai irin wannan hari a Kebbi da Katsina, yana mai cewa hakan na nuna yadda ake kuntata wa ‘yan ƙasa maimakon a basu kariya.

Martanin El-Rufai

A nasa bangaren, El-Rufai ya ce babu inda kundin tsarin mulki ya ce dole ne jam’iyya ta nemi izinin ‘yan sanda kafin gudanar da taro. Ya bayyana cewa sanar da ‘yan sanda ba doka ba ce, sai dai idan jam’iyya ta ga akwai barazanar tsaro.

See also  Har yanzu Kwankwaso bai rufe ƙofar tattaunawa da APC ba - Abdulmumin

Matsayar ‘Yan Sanda

Duk wani ƙoƙarin BBC na jin ta bakin rundunar ‘yan sanda ta Kaduna ya ci tura, domin kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan, bai amsa ba.

Masana Sun Yi Tsokaci

Masu lura da harkokin siyasa sun ce lamarin na nuna irin yanayin siyasar Najeriya, kasa da shekara biyu kafin babban zabe na 2027.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks