Da dama daga cikin ma’aikatan gwamnatin Najeriya ba su da tarbiyya – Sanusi II

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana damuwarsa kan yadda cin hanci da rashawa suka yi katutu a cikin gwamnati, yana danganta hakan da rashin tarbiyya tun daga tushe.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a daren Laraba, Sanusi ya zargi masu rike da mukaman gwamnati da rashin gaskiya da amana.
“Mutane da dama da ke cikin gwamnati ba su taso da tarbiyya ba. Mafi yawa sun shiga mulki ne saboda wasu dalilai na son rai,” in ji shi.
“An Rusa Dabi’un Kirki a Najeriya”
Sarkin ya kara da cewa ɗabi’un kirki da aka san Najeriya da su sun ruguje gaba ɗaya. Ya bayyana cewa mafi yawan shugabanni ba sa da burin barin wata kyakkyawar alama bayan mulkinsu.
“Yanzu mutane na alfahari ne da gidaje da jirage, ba wai da nagarta ko gudunmawarsu ga al’umma ba. Suna mantawa cewa mutane na kallonsu a matsayin barayi.”
Sarkin Ya Caccaki Shugabannin Addini da Sarakuna
Sanusi ya bayyana cewa ba gwamnati kaɗai ke da laifi ba, har ma da shugabannin addini da sarakuna sun shiga halin ruɗani.
“Ba shugaban ƙasa ko gwamna kaɗai ke da laifi ba. Ku duba shugabannin addini da sarakuna – kusan kowa ya fada cikin ruɗani,” in ji sarkin.
Cin hanci